Francis Peter wani nakasasshe ne da ya kwashe shekara 11 yana tafiyar kilomita uku a kan keke tdaga Kagoro a Karamar Hukumar Kaura zuwa cikin garin Kafanchan inda yake aikin gyaran rediyo a Layin Soba. A wannan tattaunawar ya bayyana yadda bambancin harkar gyaran rediyo yake tsakanin jiya da yau:
Tsawon wane lokaci ka dauka kana gyaran rediyo?
Da farko sunana Francis Peter. Shekarata 42 kuma na shafe shekara 11 ina wannan sana’a ta gyaran rediyo. Ni mutumin Kagoro ne da ke Karamar Hukumar Kaura kuma kamar yadda kake gani ina da lalura a kafata amma kullum sai na tuka keke tun daga Kagoro zuwa cikin garin Kafanchan rani da damina don zuwa wurin sana’ata.
Mene ne bambancin gyaran rediyo a da da yanzu bisa la’akari da yawaitan na’urorin satalayit da wayoyin hannu; ko mutane sun rage sayen rediyo wanda hakan ya shafi sana’arku?
Gaskiya ba haka lamarin yake ba. Ci gaban kere-kere da yawaitar na’urori kamar wayoyin hannu da sauransu bai shafi mu’amala da rediyo ba. Kanana da manyan tashoshi nawa ne za ka kama a kan wayarka ka saurara cikin natsuwa ba tare da kira ko wani abu ya katse maka abin da kake sauraro ba? Mata ma a nan yankin yanzu ne suka fi sauraron labarai a rediyo fiye da da. Maganar gaskiya ma yanzu na fi samun gyaran rediyo fiye da shekara 10 da suka wuce. Kwata-kwata nakan gyara rediyo biyu zuwa uku ne a da, amma yanzu nakan gyara rediyo bakwai ko fiye da haka a rana. Abu na biyu kuma da ya bambanta da da yanzu shi ne samuwar kayan aiki wadanda da ke yi mana wahala yanzu mukan same su cikin sauki saboda yawaitar kayayyakin China a kasuwa; amma duk da haka akwai tsada a yanzu fiye da da. Bambancin kawai shi ne tsadar rediyon wanda a da ake sayensa Naira 600 yanzu ya haura Naira dubu.
Wane alheri ka samu a cikin wannan sana’ar?
Gaskiya akwai rufin asiri sosai domin a cikinta ne na yi aure na mallaki wurin zama nake ci da iyalina hankali kwance kuma da ita ce nake daukar nauyin karatun ’ya’yana hudu.
Wane kira kake da shi zuwa ga musamman matasa kan rungumar sana’a?
Kiran da zan yi musamman ga matasa shi ne su tashi su rungumi sana’a komai kankantarta; domin nan ne rufin asiri yake. Zaman banza kwata-kwata bai yi ba, domin shi ke haifar da mutuwar zuciya har mutum ya fara tunanin aikata wani abu marar kyau. Su kuma matasan da suka yi karatu kirana gare su shi ne kada su tsaya jiran sai gwamnati ta sama musu aiki, domin jama’ar kasar nan sun fi guraben aikin kasar yawa. Wannan shi ne kirana gare su.
Ita kuma gwamnati fa?
Ita kuma gwamnati kirana gare ta shi ne idan ta ga matasa sun rungumi wata sana’a to ta yi kokari ta samo hanyoyin da za ta rika tallafa musu don dorewa da kuma ci gaban sana’ar. Misali, yanzu da nake gyaran rediyo ban kashe zuciyata ba, to kamata ya yi ta dubi ire-irenmu ta ji mene ne kukanmu, sai ta samar mana da kayayyakin aiki na zamani, idan akwai wani horo ne na zamani duka sai a ba mu sannan a kara mana jarin abubuwan da muke bukata ko da rance ne. Musamman yana da kyau ga mai aiki irin namu a ce yana sayar da kayayyakin rediyo saboda duk abin da ya mutu a jiki ya zamana muna da wanda za a saka maka ba sai mun je wajen wadansu mun saya ba ka ga ta nan za mu samu ribar kayayyakin, sannan za a biya mu kudin gyara.