Wani matashi, Ilyasu Lawal mai sana’ar sayar da kashin dabbobi da suka hada da na saniya da awaki a mahautar Kalaba da ke layin Bagobiri, Jihar Kuros riba, ya gana da Aminiya, inda ya yi bayani game da sana’arsa ta sayar da kashi, musamman yadda ta biya masa bukatu cikin shekaru 10 da ya yi a cikinta . Ya bayyana wa wakilinmu yadda yake sayar da kashin ga masu kiwon karnuka da suka hada da karnukan ’yan sanda da masu kiwo. Ga yadda hirar ta kasance:
Aminiya: Ka bayyana mana takaitaccen tarihinka.?
Ilyasu Lawal: Sunana Ilyasu Lawal.
Aminiya:Tun yaushe ka fara sana’ar saran kashi kana sayarwa?
Ilyasu Lawal: Shekara ta kai 10 ina yin wannan sana’a ta saran kashi.
Aminiya: Wane irin kashi kake sarawa ka sayar?
Ilyasu Lawal: Akwai kashi wanda muke sara wa kare, akwai kuma biscuit bone [tantakwashi]
Aminiya: Shi wannan tantakwashi da ka fada, shi ma karnuka ake ciyarwa da su ko kuwa dan Adam ma na iya amfani da shi?
Ilyasu Lawal: Eh! Mutum na iya amfani da shi a dafa shi, a yi romo ko ma miya a iya yi da shi. Wasu na sayensa suna ba karnuka, inda wasu kuma ke yin miya da shi, su ci babu wata illa.
Aminiya: Yaya maikaratu zai san bambancin tantakwashi da nau’in kashi da kake sayarwa masu kiwon karnuka?
Ilyasu Lawal:Shi irin nau’in tantakwashin ba a bai wa kare irin sa, sannan kuma shi irin wanda ake bai wa karnukan ma wasu suna iya dafa shi su tsane rowan, su sha romon sannan, su bai wa karnuka kashin. Kuma wasu na yin dafa duka da shi; ko ma duk liyafa ta annashuwa da masu gida kan yi, suna yi da shi a nan kurmi.
Aminiya: Baya ga irin wadannan, akwai nau’in kashin da ka fi kwarewa a kasuwancinsa ?
Ilyasu lawal: Shi nau’in wannan kashi ko an dafa shi an tace ruwan ba a cin sa, ko shan romonsa duka karnuka ake ba. Ina so masu karatu su fahimci cewa ko a irin kashin da muke sayarwa ga masu kiwon karnuka, suna da nau’in kashin da muke ce musu biskit bone, watau tantakwashi. Ba irin tantakwashin da mutane ke saye wurin mu ba ne suna abinci da shi.
Aminiya: To kamar da yake nan Kurmi ne su wa ye suka fi zuwa suna sayen kashin?
Ilyasu Lawal: Masu kiwon karnukan ’yan sanda, da kuma masu sha’awar kiwon kare, domin gadi, su ke zuwa suna saye.
Aminiya: Wato dai kana so mutane su gane kashin da kake sayar wa masu kiwon karnuka ba iri daya ne ba da tantakwashi da mutane ke saye suna amfani da shi?
Ilyasu Lawal: Da ma ai kashin gadon bayan shanu ne, shi kuma babu wani wanda zai iya yin amfani da shi a abinci, don haka sai masu karnuka.
Aminiya: Wannan sana’a ko tana dauke maka larurorinka ganin cewa kai magidanci ne?
Ilyasu Lawal: Alhamdulillahi na yi aure, na sanya yara na makaranta, kuma har ma ’yan uwa da abokan arziki duka gwargwadon hali ana agaza musu.
Aminiya: Wacce shawara za ka bai wa masu raina sana’a tunda kai ka ga fa’idar taka?
Ilyasu Lawal: Wannan duk shirme suke yi, duk wanda ya rike sana’a ya gode wa Allah zai samu rufin asiri. Matasa da sauran masu hali na raina sana’a a guji haka, don ba alheri ba ne; ruwan ido ko gajen hakuri duk ba ya haifar da da mai ido.