Hukumar Kula da Matasa Masu yi wa Kasa Hidima (NYSC) ta tabbatar da kamuwar matasa biyu daga cikin 826 din da aka aike zuwa jihar da cutar COVID-19.
Babbar jami’ar hukumar a jihar, Hajiya Aisha Tata ta tabbatar wa ‘yan jarida hakan jim kadan da klammala rantsar da matasan ‘yan rukunin ‘B’ zango na ’A’ a sansanin horar da matasan da ke Karaye ranar Litinin.
Ta ce an yi wa matasan ne gwajin tun kafin shigowarsu sansanin kuma tuni aka dauki matakan da suka kamata wajen ganin cutar ba ta yadu ba.
“Kamar yadda idanunku suka gane muku, mun dauki dukkannin matakan kariya kuma muna tabbatar da cewa dukkan matasan na amfani da su yadda ya kamata. Mun yi feshi domin tabbatar da cewa sansanin ya kasance a tsaftace,” inji ta.
Shi kuwa a sakonsa ga matasan, Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya yi kira gare su da su mayar da hankulansu wajen koyon abubuwan da za a koya musu a sansanin.
“Ina jan hankulanku ku kauce wa dukkan abin da zai iya shafar kyakkyawar alakar da ke tsakaninku al’ummar yankunan da kuke”, inji Ganduje.
Gwamnan, wanda Babban Sakatare a Ma’aikatar Matasa da Wasanni ta jihar, Ibrahim Ahmed ya wakilta ya ba matasan tabbacin tsaron lafiyarsu da walwalarsu iya tsawon shekara dayan da za su yi a jihar.
Daga cikin matasa 826 din da aka tura jihar dai, 387 mata ne sai kuma maza 439.