Matar mamaci, tsohon Kakakin Majalisar Jihar Edo, Hassana Garuba, da masu garkuwa da mutane suka kama awanni bayan rasuwar mijinta, har yanzu ba a ji duriyarta ba.
Bayan rade-radin cewar ‘yan bindigar sun sako Hassan a daren Asabar da suka dauke ta, wani dan uwanta ya ce mahaifiyar mamacin ce jami’an tsaro suka gani suka dauka ita ce.
“Masu garkuwa da mutane sun tafi da matar ne da direbanta suka bar mahaifiyar mamacin cikin mota”, inji shi.
Ya kuma ce ba a sace ‘ya’yan mamacin ba kamar yaddda ake cewa, saboda ba mota daya suka shigo tare da mahaifiyarsu ba.
Ya ce, da jami’an tsaro suka je inda abun ya faru sai suka tarar da tsohuwar a cikin mota suka kawo ta gida suna cewa masu garkuwa da mutane sun sako matar mamacin.
Ya kuma ce masu garkuwa da mutane sun tuntube su kan kudin fansar da za a biya amma bai bayyana nawa ne ba.
Wakilinmu ya yi kokarin jin ta bakin Kakakin Rundunar ‘Yansanda Jihar Edo, DSP Chidi Nwanbuzor, amma sai ya ce, ba shi da wani bayani saboda abun ya faru ne karkashin ikon Rundunar ‘Yansanda Jihar Kogi ne.