Matar Sheikh Ibrahim El-Zakzaky, Shugaban Kungiyar IMN wadda aka fi sani da Shi’a a Najeriya, Zeenat El-Zakzaky, ta kamu da cutar Coronavirus.
Mai magana da yawun kungiyar, Ibrahim Musa ne ya inganta rahoton a wata zantawa da ya yi da BBC Hausa.
’Yan bindiga sun sace mutane da dama a kauyen Zamfara
Sarkin Anka ya mayar da martani kan zarginsa da dakile shirin zaman lafiya
Kazalika, cikin wani rahoton da dan malamin, Sayyid Ibahim Zakzaky ya wallafa a shafinsa na Twitter ranar Alhamis, ya ce mahaifiyarsa ta kamu da cutar Coronavirus bayan likitoci sun gudanar da gwaje-gwaje domin duba lafiyarta.
Ya wallafa cewa, kwanaki shida da suka gabata bayan likitocin da ke duba lafiyar mahaifana sun ziyarce su a gidan yarin Kaduna, mahaifiyata ta yi korafin tana jin kasala da zazzabi kuma ba ta iya tantance kamshi ko wari.”
Ya ce dalilin haka ya sanya aka yi mata gwaje-gwaji cikin har na da na coronavirus inda aka tabbatar tana dauke da kwayar cutar.
Ya zuwa yanzu dai gwamnatin Jihar Kaduna ba ta ce uffan a kan wannan lamari ba ballantana na bullar cutar a gidan yarin jihar.
Tun a watan Dasumba na shekarar 2015 Sheikh Zakzaky da matarsa Zeenatu ke tsare bayan wata mummunar arangama da mabiyansa suka da wata tawaga ta Rundunar Sojin Kasa a garin Zaria.