✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jinin Nasrallah ba zai tafi a banza ba —Zakzaky

mabiya Zakzaky za su gudanar da macin nuna bakin cikin kisan jagoran na Hisbullah an Abuja.

Jagoran Harkar Musulunci a Najeriya, wadda aka fi sani da Shi’a, Sheikh Ibrahim Zakzaky, ya bayyana matukar bakin ciki da Allah wadai da kisan gillar da sojojin kasar Isra’ila suka yi wa jagoran Hizbullah Sayyid Hassan Nasrallah.

A cikin wata kakkausar sanarwa da ya fitar, Zakzaky ya bayyana kisan a matsayin ta’addanci da kisan gillar da ke nuni da Musibar Karbala, inda Imam Husaini da Sahabbansa suka yi shahada sama da shekaru dubu da suka gabata.

Ya ce, “Muna mika ta’aziyyarmu ga Limamin zamaninmu, Jagoran Jamhuriyar Musulunci ta Iran, Sayyid Ka’id, da duk masu son bijire wa zalunci a kasashen Lebanon, Falasdinu, Siriya, Iraki, Iran da Yaman.”

Ya yi alhinin rashin abin da ya bayyana a matsayin jagora wanda ya taka rawar gani a gwagwarmayar da ta shafe kusan shekaru 40.

Zakzaky ya yi tir da ‘mummunan yanayi’ da ya dabaibaye mutuwar Nasrallah, inda ya kwatanta shi da zaluncin da ba a taba ganin irinsa ba a tarihi.

Ya kara da cewa “Ba mu taba ganin irin wannan ta’asa ba a tarihinmu, kuma ba a taba ganin irinsa ba a wannan zamani namu,” yana mai cewa duk da cewa makiya da masu adawa na iya yin murnar rasuwar Nasrallah, amma farin cikinsu ba zai dade ba.

Ya kuma mika ta’aziyya ga iyalan shugaban na Hizbullah, yayin da ya yi kiran hadin kai, da bukatar al’ummar Musulmi da ta zabi tsakanin ‘zalunci ko bijirewa masa.’

Sai dai Zakzaky ya bayyana kwarin gwiwar cewa za a dauki fansa kan shahadar Sayyid Nasrallah, sannan za a yi adalci ga dukkanin al’ummar da aka zalunta, yana mai cewa “Jinin Sayyid Nasrallah ba zai tafi a banza ba.”

A Agustan 2022, marigayi Nasrallah ya aika sakon jajantawa ga Zakzaky da ma sauran mabiyansa a Najeriya kan kashe wasu masu muzaharar Ashura a shekarar da aka zarg jami’an tsaron Nijeriaya da aikatawa.

Kwana guda bayan kashe shugaban na Hisbullah, wasu mabiya Zakzaky suka gudanar da maci a wasu garuruwa da ma biranen a Arewacin Nijeriya domin nuna bacin rai game da kisan Nasrallah.

Sai dai Aminiya ta jiyo daga kakakin mabiya Zakzakyn cewa sai a yau Jumma’a ne za su gudanar da macin nuna bakin cikin kisan jagoran na Hisbullah an Abuja.