Matar mahaifin Gwamnan Jihar Bauchi, Alhaji Bala Muhammad Abdulkadir (Ƙauran Bauchi), Hajiya Hauwa Duguri, da aka fi sani da Dada ta rasu tana da shekara 120 a duniya.
Rasuwar Hajiya Hauwa, wadda aka bayyana a matsayin babban rashi, ba wai kawai ga iyalanta ba har ma ga al’ummar Jihar Bauchi baki ɗaya.
- Mota ta kutsa cikin mutane ta kashe 10 a Amurka
- Tinubu ya shafe kwanaki 180 daga cikin 580 da ya yi na mulkinsa a ƙasar waje – Obi
Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, wanda shi ne Shugaban Ƙungiyar Gwamnonin Arewa, ya miƙa ta’aziyyarsa ga Gwamnan Bauchi bisa wannan babban rashin.
A cikin wata sanarwar ta’aziyya da Babban Daraktan Yaɗa Labarai na Gidan Gwamnati Jihar Gombe, Isma’ila Uba Misilli, ya fitar a madadin Gwamna Inuwa Yahaya ya bayyana rasuwar a matsayin babban giɓi mai wuyar cikewa.
Gwamna Inuwa Yahaya ya ce Hajiya Hauwa ta kasance uwa mai hangen nesa, wadda ta yi shekaru masu albarka a duniya, kuma ta zama abin koyi ga al’umma.
Ya ƙara da cewa, rasuwarta ta zo ne a lokacin da ake matuƙar buƙatar shawarwarinta na hikima.
Ya kuma yi kira ga iyalan marigayiyar da su rungumi ƙaddara, tare da yin koyi da kyawawan ɗabi’un da ta bari a baya.
A ƙarshe, Gwamnan ya yi addu’ar Allah Ya gafarta mata, ya yafe mata kura-kuranta, sannan ya sanya ta cikin gidan Aljannah Firdausi.