✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Matar Gwamnan Kebbi ta yi zarra a fannin kula da lafiya

A yau idan akwai wata matar gwamna a duk fadin yankin Arewa koma daukacin fadin kasar nan da za a iya bai wa kambin yabawa,…

A yau idan akwai wata matar gwamna a duk fadin yankin Arewa koma daukacin fadin kasar nan da za a iya bai wa kambin yabawa, godiya da  jinjinar ban girma,to ba za ta wuce Dokta Zainab Atiku Bagudu (matar Gwamnan Jihar Kebbi) ba. Wannan mata  jaruma ce, hazika ce hadima ce, domin ko ba komai ta taimaka wa mijinta, ta  kuma taya shi fita kunyar talakawansa.

Koda yake barewa ba ta yi gudu danta ya yi rairafe ba, domin Zainab Bagudu ‘ya ce ga Alhaji Ummaru Aliyu shinkafi (marafan sokoto), wanda kowa yasan shi babban Jarumi ne a ma’aikatar ‘yan sandar ciki,wanda ya rike mukamin babban darekta a ma’aikatar tsaro ta Najeriya. Mahaifiyarta kuwa babbar lauya ce da ta amsa kiran mukamin lauya tun cikin shekaru fiye da talati da suka gabata.

Bayan kammala karatun sakandare  a kwalejin  sarauniyya (Queens Collage)  da ke Legas a cikin  shekarar 1984,  Zainab Shinkafi ta yi nasarar fara karatu a jami’ar Ahmadu Bello da ke zariya, a inda ta yi digirinta na farko a fannin likitan mutane. Bayan nan kuma ta tafi Ingila dake kasar Birtaniya domin yin karatun kwarewa a fannin likitan Yara, inda har wa yau ta sake yin digiri na biyu a fannin likitan yara. Ta kuma kara yin difiloma a Royal College da ke Ingila don kara samun horo na musamman akan lafiyar yara da kuma zamowa daya daga cikin mambobin kungiyar likitocin yara na duniya.

Bayan dawowarta gida Nijeriya a shekara ta 2002, Hajiya Zainab Bagudu ta riki mukamin babbar jami’a mai kula da sashen kananan yara na asibitin Garki da ke binnin tarayya Abuja. A shekara ta 2009 ne Likita Zainab ta fara shirinta na tsere sa’anni, domin ta kirkiro wata Cibiya da ake kira da suna ‘Medicaid cancer foundation.’  Medicaid cibiya ce da aka ginata ta musamman don duba lafiyar al’umma, tare da taimakon nagartattun na’urori, domin an cikata makil da na’urorin binciken ciwwuka iri-iri, kuma wadanda suke tafiya tare da zamani(na’urorin). Akwai irin su MRI(na’urar hoton sassan jiki na ciki),CT scan(na’urar akwatin da ake saka mutum don ganin hoton dukkanin cututtukan da ke jikinsa), Endoscopy(na’urar gano cututtukan da ke cikin hanji da tace su),Echocardiology(na’urar auna bugun zuciya da matsayin lafiyarta) da dai sauransu da dama da ba mu anbata ba. Sannan a cibiya ce mai zaman kanta da ake duba lafiyar kananan yara.

Hajiya Zainab, zamowarta matar babban gwarzon dan kishin kasa,watau Alhaji Abubakar Atiku Bagudu, tun yana Sanata har zamowarsa Gwamnan Jihar Kebbi a yau, ya ba ta dama, ya kara mata azama da zimmar ganin ta kusantu ga talakawa, kamar yadda ta dade tana cin burin ganin ta yi hakan, watau  bayar da gagarumar gudunmawa ga ingata lafiyar rayuwar talaka, musamman mata da kananan yara, da kuma tallafa wa matasa a hanyoyin cigaban rayuwarsu.

Gaskiya Hajiya Zainab Allah ya cika mata burin yin wani abun  alfanu ga al’ummarsa. 

 Abin da ya sa muka anbata hakan kuwa shi ne,idan ka yi duba da irin tarin tulin ayukan ci gaban al’ummar kasar nan da take aiwatarwa musamman ga jama’ar jihar Kebbi da kuma na jaharta ta haihuwa watau jihar Sokoto abin sai wanda ya ji ya gani. 

Mu dauki misali da wannan shekara ta 2017 kadai mu gani, tun daga farkonta (watan Janairu) har zuwa wannan wata na Disamba(karshen shekara), ba a samu wani wata da Dokta Zainab Bagudu ta tsaya don ta huta daga yi wa jama’a hidima ba. Aikin ke nan kaddamar da ayukan ci gaban al’ummar Jihar Kebbi da Jihar Sakkwato da Binnin Tarayya Abuja, ko kuma dai wata jiha har shekarar ta kare. Wasu ayyukan da ta kaddamar a bana shaida ne na cewar Zainab Bagudu ce  Jarumar Matan Gwamnonin Qasar nan, ga ayukan a jere kamar haka:- 

Dokta Zainab Bagudu ita ce matar gwamna ta farko a kasar nan da ta kaddamar da yekuwa akan fahimtar gane cutar Daji(cancer) a duk fadin kasar nan. A cikin shekarar nan ce ta kaddamar da cibiyarta ta Medicaid a garin Birnin kebbi,babban birnin jihar Kebbi. Ta kaddamar da ba da horo na musamman ga ma’aikatan lafiya a Jihar Kebbi akan sanin yanda ake gane mata masu dauke da cutar dajin nono da ta mahaifa. An tace mata fiye da dubu biyu masu dauke da cutar, kuma an tallafa masu da ba su magani, ko yi musu aikin fida ga wadanda yanayin jikinsu ya bukaci hakan. Ta kirkiri kungiyoyin yekuwar gane cutar daji a daukacin makarantun gaba da firamare na fadin jihar. 

Matar gwamnar jihar Kebbi ta karfafa zukatan matan jihar da su koma gona,a inda ta fara wannan aikin nata da kananan hukumomi hudu na jihar. Ta kai masu taki da iraruwa,ta basu kudaden fara aiki, ta kuma hadasu da malaman gona mashawarta.

Matar gwamna mace ce mai tausayi domin ko a cikin watan uku na wannan shekarar, tana tafiya ta ci karo da wata mata marar hankali (mahaukaciya) tare da ‘yarta Siddika,nan da nan tausayinta ya kamata ta sa aka dauki matar zuwa asibiti, yarinya Siddika kuwa ta nufi gidanta da ita,aka sakata makaranta ana kiran yarinyar da suna Siddika Bagudu.

A kowace shekara cikin watan Azumi sai ta shirya taron wa’azi, don ilmantar da al’umma, tare da kara dankon zumunci da tallafa wa juna a tsakanin ‘yan jihar.

A gaskiya ayyukan Hajiya Zainab Bagudu sun sa ta yi zarra fannin kula da lafiya da tarairayar rayuwr al’umma.

Ba mu ce tafi kowa ba, amma tasirin ayyukanta sun taba rayuwar talakawan jiharta. Mun gode Allah. Aisha Usman Liman 09093467171