Uwar gidan Gwamnan Jihar Kano, Farfesa Hafsat Umar Ganduje ta bukaci a sanya gwajin miyagun kwayoyi a cikin jerin gwaje-gwajen da za a rika yi wa ma’aikatan da gwamnati za ta dauka aiki a jihar.
Ta yi wannan kiran ne a taron bikin Ranar Yaki da Shan Miyagun Kwayoyi ta Duniya ta 2021 da ya gudana a Jihar ranar Asabar.
- Najeriya za ta fara karbar haraji daga ribar Google da Twitter – Osinbajo
- Bayan wasanni 18 an doke Akwa United a Firimiyar Najeriya
Mai dakin Gwamnan ta bayyana damuwarta kan yadda shan miyagun kwayoyi ke ci gaba da yin barazana ga yaruwar al’umma.
Ta kuma bukaci iyaye da masu sarautun gargajiya da su dage wajen yaki da muguwar dabi’ar.
Daga nan ta bukaci a shirya wayar da kan al’umma zuwa gida-gida kan illar shan miyagun kwayoyi saboda mata iyaye su samu damar bayar da tasu gudunmawar wajen yakin.
Tun da farko dai, Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Kasa (NDLEA), a Jihar Kano, ta koka kan yadda take da karancin cibiyar gyaran hali, duk da alkawarin da Gwamnatin Jihar ta yi mata na kammala wasu da ake kan ginawa.
‘Kano ta ce ta 6 a cikin jihohin da aka fi ta’ammali da miyagun kwayoyi’
Da yake nasa jawabin, Shugaban Kwamandan NDLEA a Jihar Kano, Isa Mohammed Likita, ya bayyana cewar Jihar ta sauko kasa daga jerin jihohi da aka fi samun masu amfani da miyagun kwayoyi a Najeriya.
Sai dai duk da haka, ana ci gaba da samun matasa da ke ta’ammali da kwayoyin, wanda a yanzu suka canza salo na shan wasu magungunan gargajiya da sunan shaye-shaye.