Matar da aka fara yi wa dashen fuska a duniya, Isabelle Dinoire ta rasu, kamar yadda likitoci a kasar Faransa suka bayyana shekaranjiya Laraba.
Sanawar da asibitin Amiens Hospital, wurin da aka yi mata aikin dashen fuskar a watan Nuwamban shekarar 2005, ya fitar, ta ce Isabelle ta rasu ne ranar 22 ga watan Afrilun da ya gabata, bayan doguwar jinya. Ta rasu tana da shekara 49 a duniya, kamar yadda kafar labarai ta CNN ta bayyana. Asibitin ya ce dalilin bayyana labarin rasuwarta a makare, ya samo asali ne daga wasiyyar da marigayiyar ta bari, wadda ta bukaci kada a bayyana labarin rasuwarta ga manema labarai.
Sai dai asibitin bai bayyana ciwon da ya yi ajalinta ba. Kodayake, kafafen labaran kasar Faransa sun ruwaito cewa rashin lafiyar da ya yi ajalinta yana da nasaba da aikin dashen fuskar da aka yi mata a baya.
An yi wa marigayiyar aikin dashen fuskar ne lokacin da take da shekara 38 da haihuwa, bayan karyarta ta cije ta a fuska. An dasa wa marigayiyar wani bangare na fuskar wata mace da ta kashe kanta ne.
Kuma shekara guda bayan aikin ne, Dinoire ta ce: “Fuskar nan ba tawa ba ce, amma duk lokacin da na dubi madubi, kaina nake gani.”
Aikin da aka yi wa marigayiyar a kasar Faransa ya bude hanyar fara yin dashen wasu sassan fuskar dan Adam a wasu kasashe shida, ciki har da kasar Amurka.
Matar farko da aka yi wa dashen fuska a duniya ta rasu
Matar da aka fara yi wa dashen fuska a duniya, Isabelle Dinoire ta rasu, kamar yadda likitoci a kasar Faransa suka bayyana shekaranjiya Laraba.Sanawar da…