Masu iya magana sun ce mahakurci mawadaci, wannan shi ne abin da ya faru da iyalan Mista Sabastine Pyoklam da ke Karamar Hukumar Jos ta Kudu a Jihar Filato inda matarsa Misis Manji Sabastine Pyoklam ta haifi ’ya’ya hudu rigis bayan sun shafe shekara bakwai da suna neman haihuwa ba su samu ba.
Misis Manji ta bayyana wa Aminiya cewa ta samu kanta cikin mamaki da jin dadi lokacin da ta haifi ’ya’ya hudu – biyu maza, biyu mata ba tare da wata matsala ba.
Mai jegon wacce suka yi aure da mijinta Sabastine Pyoklam Jibrin a shekarar 2011, ta ce sun shafe shekara bakwai ba tare da ta haihu ba, inda ita da mijin suka yi ta fadi-tashi hade da addu’o’i don ganin sun samu haihuwa.
Ta ce abin mamaki da annashuwa shi ne, a bara sai ta samu juna biyu. Ta ce da ta sanar da mijinta cewa tana dauke da juna biyu bai yarda ba, har sai da suka je wani asibiti a garin Jos, inda bincike ya nuna cikin ’yan hudu take dauke da shi.
Labarin tabbatuwar cikin ya sanya ita da mijinta cikin nishadi da jin dadi, inda suka fara zumudin zama iyaye. Ta ce daga baya fargaba ta lullube su saboda rashin sanin abin da zai iya zuwa ya dawo.
Misis Manji ta ce daga baya sun fawwala wa Allah dukkan al’amuransu saboda a cewarta Shi ne Ya sanya ta kai shekara bakwai da aure ba ta samu ciki ba, don haka lokacin da Ya ga dama Ya ba ta, to zai sanya ta haihu ba tare da wata matsala ba, kuma hakan ya faru.
Aminiya ta gano cewa Misis Manji da Sabastine sun yi aure ne a ranar 19 ga Nuwanba, 2011. Kuma rashin haihuwa ya sa suka ci gaba da addu’a, “Allah Ya jikanmu Ya sanya na samu ciki na haifi ’yan hudu maza biyu mata biyu ta hanyar tiyata a ranar 9 ga Fabrairu, 2019,” inji ta.
Ta ce, lokacin da take goyon cikin, ita da mijinta sun samu kansu cikin fargaba, “Saboda ba mu san abin da zai je ya zo ba, amma a karshe Allah Ya sa na haifi ’ya’ya hudu rigis kuma cikin koshin lafiya. Lokacin da aka ce na haihu sai na bukaci in ga ’ya’yana, inda daya bayan daya na dauke su, na kuma gan su” inji ta.
Misis Manji mai kimanin shekara 33, ma’aikaciyar Gwamnatin Jihar Filato ta ce ita ce mace ta farko da ta taba haihuwar ’yan hudu a jihar.
“Duk da cewa mahaifiyata ta haifi ’yan biyu, amma a cikin danginmu da ma Jihar Filato a iya sanina ni ce mace ta farko da ta haifi ’yan hudu. Wannan abin jin dadi ne da godiya ga Ubangiji,” inji ta.
Ta ce, abin da ya fi kara sanya ta cikin farin ciki shi ne yadda ta yi goyo da rainon cikin ba tare da laulayi ba, “Sai dai na yi kwadayi sosai, domin komai na gani ina so in ci, kuma ban rika amai ko samun tashin zuciya ba, na dai yi ciye-ciye,” inji ta.
Mijinta Sabastine Pyoklam Jibrin ya ce, farin ciki a wurinsa lokacin da matarsa ta haifi ’yan hudu ba zai misaltu ba.
Ya ce, “Lokacin da matata ta fada mini tana dauke da juna biyu na yi farin ciki, sai na ce mu je asibiti, bayan mun je an yi bincike ne sai likita ya fada mana cewa ai tana dauke da ’yan hudu. Na yi mamaki sosai, na samu kaina cikin al’ajabi.”
Sabastine wanda dan kasuwa ne kuma malami a Kwalejin Lafiya da ke Zawan a Jihar Filato ya ce, daga nan shi da matarsa suka rika addu’a, “Kuma cikin ikon Allah aka yi goyon cikin lafiya, domin ba a rika samun laulayi ba, kuma duk lokacin da muka je awo asibiti sai likita ya ce mana komai lafiya,” inji shi.
Ya ce, a lokacin goyon cikin likita ya shawarci matarsa ta kwanta a asibiti, amma saboda rashin kudi ya sanar da shi hakan ba zai yiwu ba, sannan ya fada wa matarsa cewa Allah Zai lura da cikin har ta haihu lafiya.
Ya ce, likitan bai ji dadin haka ba, inda ya bukaci su rika zuwa asibitin a-kai-a-kai don a rika lura da halin da cikin ke ciki.
“Haka muka ci gaba da zuwa asibiti har tsawon wata shida zuwa bakwai, inda bara zan je bikin Kirsimeti a kauye sai na ce bari in kai ta asibiti gudun abin da zai iya faruwa idan ba na nan. Na kai ta asibitin ne ba wai don ba ta da lafiya ba, saboda ko a lokacin tana iya dafa abinci da sauran aikace-aikacen gida,” inji shi.
Ya ce lokacin da ya kai ta asibitin, likitan ya nemi ya yi mata tiyata a ciro ’ya’yan amma ya ki amincewa domin matarsa ba ta jin wani ciwo dangane da cikin.
Ya ce, “Ganin ban amince a yi tiyata ba sai likitan ya sanar da mu cewa mu zo asibiti duk lokacin da muka ga ta fara laulayi don a yi mata tiyata, amma har tsawon wata takwas ba ta yi wani laulayi ba. Abu dai ya tafi kusan wata tara, inda a nan ne aka yi mata tiyata aka ciro ’yan hudun, saboda sun kosa don haka ba a sa su a wata na’ura ba.”
Ya ce, har zuwa yanzu ’yan hudun suna cikin koshin lafiya sai dai lura da su yana bukatar kashe kudi sosai. “Tunda aka haife su ni nake lura da su, babu wani tallafi daga gwamnati. Don haka muna bukatar taimako daga gwamnati da kungiyoyi masu zaman kansu da sauran masu hali.”