✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Matar da ke kai wa ’yan bindigar Zamfara makamai ta shiga hannu

An cafke wanda ya kitsa garkuwa da maihfiyarsa, an kwace layikan waya 1,000 a hannun wasu ’yan ta’adda

Dubun wata mata mai yi wa ’yan bindiga safarar makamai a Jihar Zamfara ta cika, bayan da ’yan sandan suka cika hannu da ita.

Kazalika, ’yan sandan jihar sun cafke wasu mutum 12 da ake zargi masu garkuwa da mutane ne a jihar dauke da layin waya guda 1,000.

Cikin sanarwar da ya fitar a Gusau, babban birnin Jihar Zamafara, mai magana da yawun ’yan sandan jihar, SP Mohammed Shehu, ya ce kamen nasu ya hada da wani da ya yi ikirarin yin garkuwa da mahaifiyarsa.

A cewar Shehu, matar da aka kama ta kware wajen yi wa ’yan bindiga safarar bindigogi da alburusai a Jihar Zamfara.

Inda ya ce tana gudanar da harkokinta ne tsakanin Jihar Nasarawa da Zamfara.

Ya ce sun kwato bindigogi kirar AK 47 da alburusai da dama daga hannunta.

“A ranar 13 ga Fabrairu jami’an ’yan sanda suka kama matar dauke da alburusai 325.

“Kamen nata ya biyo bayan bayanan sirrin da aka samu game da zirga-zirgarta na yi wa ’yan bindiga safarar makamai a dajin Zamfara daga Lafiya a Jihar Nasarawa.

“Ta fada mana cewa da fari, ta yi wa barayi a jihar safarar bindiga kirar AK47 guda uku da alburusai 1,000,” in ji Shehu.

Ya ce za a gurfanar da ita a kotu nan ba da dadewa ba.

Ya kara da cewa, masu garkuwar da aka kama su ne masu addabar mutane a wasu sassan Kaduna da Kano da sauran jihohi makwabta.