’Yan sanda sun damke wani basarake da zargin yi wa ’yar cikinsa mai kimanin shekaru 15 fyade.
Basaraken shi ne Baale na Masarautar Oose Agbedu Ajibawo da ke Owode-Yewa a Karamar Hukumar Yewa ta Jihar Ogun.
Yarinyar ce ta kai karar mahaifin nata wurin ’yan sanda na Owode Egbado inda ta ce tun tana da shekaru 11 yake lalata da ita kuma sakamakon haka ne ta samu matsala a mafitsararta.
Kakakin ’yan sandan jihar, Abimbola Oyeyemi ya ce bayan nan ne DPO na yankin Owode-Egbado, SP Olabisi Elebute ya tura jami’ansa suka cafko dagacin.
“Ta shaida mana cewa mahaifiyarta ta rasu tun tana da shekaru biyu, amma mahaifinta ya ki ba dangin mahaifiyarta ita, ya kuma yi amfani da damar wajen lalata ta”, inji kakakin.
Oyeyemi ya ce da farko basaraken ya musanta zargin, amma da tsohuwar matarsa ta tabbatar da abun da yarinyar ta fada, nan take ya fadi sumamme aka kai shi asibiti ya farfado.
“Tsohuwar matar tasa ta shaida wa jami’anmu cewa ta kama shi yana lalata da diyar tasa, wanda ta ce shi ne dalilin rabuwa da shi saboda takaici”, inji kakakin ’yan sandan.
Tuni aka hannanta yarinyar ga gidan marayu na Stella Obasanjo domin ci gaba da samun kulawa.
Oyeyemi ya ce kwamishinan ’yan sandan jihar, Edward Ajogun ya umarci a tsare wanda ake zargin a bangaren yaki da safarar mutane da bautar da kananan yara na Sashen Binciken Manyan Laifuka na rundunar domin zurfafa bincike da kuma gurfanar da shi a kotu.