✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Matar aure ta kashe dan kishiyarta

Ta dura wa dan amaryarta guba saboda miji ya fi damuwa da ita

Wata matar aure ta amsa cewa ta kashe dan kishiyarta ta hanyar ba wa karamin yaron guba, saboda mijinta ya fi son uwar yaron.

Matar, wadda ke dauke da juna biyu ta ce ta dura wa dan amaryarta maganin kwari ne a lokacin da ya baro wurin uwar tasa ya shigo dakinta a ranar da abin ya faru.

“Son zuciya da kishi ne suka sa na kashe dan kishiyata. Danta daya kuma ban jin dadin yadda mijina ke nuna mata kulawa fiye da ni,” inji mai cikin.

Matar mai shekara 24, ta kuma bayyana bacin ranta cewa uwar yaron, wacce ita ce amarya kuma ’yar gaban goshin mijinsu, ba ta girmama ta.

Wadda ake zargin ta ce bayan ta aika yaron lahira ne ta yi da-na-sanin abin da ta aikata, kuma ita da kanta ta gaya wa mijinta abin da ta aika.

Wannan matar aure wadda kuma take sana’ar dinki na cikin mutum 12 da ’yan sanda suka gabatar bisa zargin aikata manyan laifuka a Jihar Osun.

Sauran wadanda ake zargin da Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar ya gabatar sun hada da mutum biyu da ake zargi sun yi garkuwa da fasinjoji 12 a cikin wata mota.

Akwai kuma wasu mutum hudu da aka kama bisa zargin aikata kisan kai, hada baki da kuma sayar da sassan jikin dan Adam a garin Iwo; da sauransu.