Hajiya Fatima, uwargidan Ɗan Majalisar Tarayya mai wakiltar mazaɓar Bauchi ta Tsakiya, Aliyu Aminu Garu, ta sha suka a kan raba sandunan rake ga wasu matasa a matsayin wani shiri na ƙarfafa gwiwa kan sana’o’i.
Hotunan taron ƙaddamar da ƙarfafa gwiwar sun janyo izgilanci da suka ga matar ɗan majalisar la’akari da halin da ake ciki.
- ’Yan bindiga sun sace mata 4 a asibiti a Katsina
- NAJERIYA A YAU: Yadda Mazauna Maiduguri Za Su Kubuta Daga Illolin Ambaliya
Jam’iyyar PRP reshen jihar Bauchi ta nuna rashin jin daɗinta game da lamarin.
A cikin wata sanarwa da sakataren jam’iyyar PRP na jihar Abdulazeez Haruna ya fitar, ya ce, “Wannan karamcin ya yi ƙasa da yadda ake tsammanin wakilci nagari ga al’ummar mazaɓar tarayya ta Bauchi.
“A matsayinmu na jam’iyya, mun yi imanin cewa wakilci na gaskiya ya wuce irin wannan ƙarfafawar gwiwar ga matasan.
Jama’ar Ƙaramar Hukumar Bauchi/Mazaɓar Tarayyar sun cancanci fiye da hakan. Sun cancanci dabarun ci gaba masu ma’ana waɗanda ke magance matsalolin buƙatu da damuwar matasan.
“Muna kira ga Honorabul Aliyu Garu ya yi la’akari da ayyukansa da wanda ba ayyukansa ba a majalisar dokokin ƙasar.
“Musamman muna buƙatar sanin irin ayyukan cigaban da ya kawo wa al’ummar ƙaramar hukumar Bauchi tun bayan zaɓensa.
“Daftarin doka nawa ya gabatar waɗanda suka yi tasiri ga rayuwar mutane?
“Waɗanne ayyuka na zahiri da ya ɓullo da su ko kuma ya tallafa don inganta walwala da rayuwar al’ummar mazaɓar?”