✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Matan Kannywood sun yunkuro domin samar da hadin kai a tsakaninsu

A ranar Asabar ce wasu daga cikin jiga-jigan matan da ke cikin masana’antar fina-finan Hausa ta Kannywood, suka bayyana yunkurin da suke yi domin samar…

A ranar Asabar ce wasu daga cikin jiga-jigan matan da ke cikin masana’antar fina-finan Hausa ta Kannywood, suka bayyana yunkurin da suke yi domin samar da hadin kai da taimakon juna a tsakaninsu.

Wannan yunkuri dai ya kai ga kafa wata sabuwar kungiya da suka sanyawa AKAFA, wato kungiyar Matan da ke bada gudummawa a masana`anar ta Kannywood, kumamka kaddamar da ita a ranar Asabar din.

Kungiya ce da manyan jarumai tsoffi da sabbi irinsu Rashida Adamu da aka fi sani da Rashida Mai Sa`a, da Mansura Isa,da Muhibbat Abdussalam, da Halima Atete, da Hajiya Maryam Sulaiman da aka fi sani Da Maryam CTV, su ka jagoranci kafawa da kaddamar da ita.

Jarumai da dama da aka jima ba a ga fuskokinsu ba sun halarci wannan taro, yayin da wadanda ludayinsu ke kan dawo su ma ba a bar su a baya ba.

Aminiya ta tattauna da dama daga cikin wadannan jarumai da ma jagororin kan wannan haduwa da suka shirya, da zummar  samawa kansu mafita kan matsalolin da ke addabar masana`antar bangaren mata.

Su waye suke jagorancin kafa AKAFA?

Hajiya Rashida Adamu mai Sa`a wacce ta taba rike mukamin mai ba wa Gwamnan Kano shawara ta musamman kan harkokin mata, ita ce shugabar kungiyar, ta kuma ce sun kafa ta ne da zummar samar da hanyar sada zumunci a tsakaninsu matan Kannywood din, baya ga zamowarta hanyar share wa juna hawaye a duk sanda bukatar hakan ta taso.

Ta ce “wannan taron mun shirya shi ne don zumunci da kuma tallata kungiyar mu ta AKAFA ga duniya, da ita za mu cigaba da hada-hadar mu, da nemo ayyuka daga `yan siyasa da masu kudi,  hadi da kungiyoyi, har ma daga aljihunmu domin tallafawa `ya `yan kungiyar ta mu. Dukkanmu mata ne kuma in sha Allahu da taimakon mataimaka na su Muhibbat Abdussalam, da Mansura Isah, da Halima Atete, da Samira Ahmad, za mu tabbatar da kungiyar nan ta tattaro kowa da kowa an tafi tare da sh, saboda ko a yanzu mun tattaro tsoffi da sabbin jarumai wasu tun in akarama nake kallonsu a Talabijin yau ga shi mun hada ana raha da zumunci”.

A na ta bangaren sakatariyar kungiyar Muhibbata Abdus Salam cewa ta yi “ wasunmu na da aure, wasu furodusoshi ne, wasu kuma kasuwancin su su ke yi yanzu. Kumadole sai da zumunci za mu san matsalolinmu sannan mu san maganinsu, ba kuma wai lallai sai da kudi ba, magana mai dadi ma na kara dankon zumunci”.

“Kinga kamar kwanakin baya yadda wani ya ci mana mutunci da suanan waka, amma da jagororinmu suka yunkuro sai suka kwato mana `yancinmu, yanzu so muke mu yiwa kan mu wannan gatan. Kuma za mu tafi da kowa da ke son mu yi masa aiki musamman `yan siyasa, ke ko dan sarkin Saudiyya ya ce mu zo mu yi masa aiki a shirye muke don yin hakan”.

a nata bangaren shugabar tsare-tsaren kungiyar Mansura Isah ta ce wannan kungiya ita ce irinta ta farko da aka taba kafawa a Kannywood, kuma sun kafa ta ne domin karfafa zumunci a tsakininsu, da kuma kawo karshen matsalolin junansu ba tare da samun musayar yawu a tsakanin jaruman a kafafen sada zumunta ba kamar yadda aka saba gani a baya.

Ta ce “kungiyar nan don  gano matsalolin mu ne muka kafa ta, da kuma tallafawa juna da dan abinda muke da shi, za mu hada karfi da karfe domin sharewa juna hawaye. Kamar yadda kike gani wasunmu duk da sun bar taka rawa a masana`antar amma muna da abubuwan yi da suka samar mana rufin asiri”.

Da ta ke amsa tambaya kan hanyoyin da za su bi don kawo karshen kalubalantar juna da matan Kannywod din kan yi a kafafen sada zumunta idan sun samu sabani, Mansura ta ce dama duk in da `yan uwa suka taru sai an samun sabani, amma dai za su yi kokarin ganin an warware ba tare da yiwa juna terere a kafafen sada zumunta ba.

Hajiya Maryam Sulaiman wacce aka fi sani da Maryam CTV, ta ce a matsayinta na mataimakiyar shugabar Kungiyar AKAFA, ta na ganin kungiyar za ta kawo cigaba ga kowacce `yar Kannywood domin ta tsaya da kafafunta, kuma tuni alamun nasara suka bayyana ga kungiyar, kasancewar mata a masana`antar ba su taba shirya irin wannan taro ba a  baya.

“Kasancewar shugabar mu macece mai jajircewa, mai akida mai kyau wacce ta san darajar mata , shi ya sa ma mata suka amsa kira suka yo fitar dango tun daga tsoffin jarumai, da ma wadanda suka yi aure suka halarta”.

 

SAURAN MAMBOBI

Wata jarumar da ta shafe shekaru masu tsawo ba a ji duriyarar ta ba tun bayan aurenta da Dan Margayi Sarkin Kano Ado Bayero mai suna Bello Ado Bayero, wato Maijidda Ibrahim ta ce tayi matukar farin ciki da kafa wannan kungiyar ta AKAFA, kuma suna sa rai za ta samar da dorewar zumunci a tsakaninsu, musamman irinsu da su ka rufe kofartaka rawa a masana`antar saboda  igiyar aure.

Ita ma wata jaruma  da ke tashe a yanzu a masana`antar wato Samha M Inuwa ta ce “ kungiyar ta taimakon kai da kai ace da suke fatan tunda ta kunshi sabbi da tsoffin jarumai su kari juna da ilimin da su ke da shi da kuma dan abinda su ka mallaka, domin dai babban dalilin kafa tan kenan.

“Ana so ne  a samar mana cigaba da kuma hanyar tallafawa juna cikin sirri ba tare da wani ma a waje ya sani ba”, in ji ta.

Aminiya dai ta ci karo da jarumai da dama tsoffi da sababbi da `ya `yanyensu da suka hada da Yahanasu Sani, Hadiza Kabara, Sadiya Gyale, da Ladin Cima, Hajiya Asma`u, da kuma da dama daga jaruman wasan kwaikwayon Dadin Kowa da Kwana casa`in na Arewa24.