✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Matan Hadaddiyar Daular Larabawa na adana kwansu har lokacin da suke son haihuwa

Mata da dama a Hadaddiyar Daular Larabawa na adana kwayayansu zuwa lokacin da suke bukatar haihuwa, musamman saboda sukan dade ba su yi aure ba.…

Mata da dama a Hadaddiyar Daular Larabawa na adana kwayayansu zuwa lokacin da suke bukatar haihuwa, musamman saboda sukan dade ba su yi aure ba. Likitoci dai sun ce fasahar kimiyyar adana kwayayen haihuwa za ta ba su damar haihuwa ko da sun jinkirta lokacin aure.
Adana kwayayen haihuwa na ta karuwa, kuma mata ba suna zabar yin haka ba ne saboda kula da lafiya, al’amarin da ya hada da yin maganin cutar daji, a’a, suna ma yin hakan ne bisa dalilan zamantakewa ko wasu dalilai na kashin kansu.
Dokta Monika Chawla, wata kwararriyar likita kan al’amuran haihuwa da ke Cibiyar kyankyasar kwayaye ta Fakih IbF Fertility Centre a birnin Abu Dhabi, ta bayyana wa jaridar Khaleej Times cewa, mata ba su bukatar yin aure da wuri ko aure ya kawo musu cikas (rashin haihuwa) saboda nisan shekaru.
“Adana kwayayen haihuwa abu ne mai yiwuwa, don haka ba za a kayyade wa mata lokaci ba,” inji ta.
Dokta Chawla ta yi nuni da cewa mata a Hadaddiyar Daular Larabawa na tsoron rashin haihuwa saboda nisan shekaru, musammman ma saboda mafi yawan matan a wannan zamani suna yin aure bayan shekarunsu sun ja da yawa.
A cewarta: “Mata na iya adana kwan haihuwarsu har zuwa lokacin da suka samu mijin da ya kwanta musu ko kuma suka shirya haihuwa da rainon ’ya’ya a lokacin da ba za su kawo musu cikas a aikin ofis ko wasu harkokin rayuwa ba.
Ta yi bayanin cewa, bayan wasu shekaru idan mace ta shirya haihuwa, za a yi amfani da wanda nisan shekarunta ba zai kawo mata cikas ba, har ya kyankyashe ta samu ta haihu.
Ana danganta nasarar ce da fasahar kimiyyar daskarar da ruwa-ruwa ya koma tamkar gilashi ko kankara, dabarar da yanzu ake aiwatar da ita a kan kwayayen haihuwa, cewarta.
“Fasahar kimiyyar adana kwayayen haihuwa ta fito ne cikin shekara 10, kuma ana amfani da ita ne saboda dimbin nasarar da aka samu a gwaje-gwajen da aka yi,” inji ta.
Dokta Chawla ta yi nuni da cewa, wannan sabuwar kimiyyar na da tabbacin samun nasara da kashi 80 zuwa 85, in an kwatanta da tsohuwar fasahar da ake amfani da ita, wadda aka cimma kashi 50 cikin 100. Kuma saboda rashin iya daskarar da kwayayen cikin sauri, amfani da kwan wajen daukar ciki ba shi da tabbas.
kwararriyar likitar ta karkare bayananta da yin nuni da cewa, binciken kimiyya na dada fadada, don haka mata su kwantar da hankalinsu ko da sun jinkirta haihuwa, domin suna da damar kasancewa uwa.