✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Matan da ke yin fim ba karuwai ba ne – Fati Karmatako

 Aminiya ta samu tattaunawa da fitacciyar jaruma Fatima Yusuf wacce ake yi wa lakabi da Fatima Karmatako. Ta bayyana dalilan da suka sanya ta shiga…

 Aminiya ta samu tattaunawa da fitacciyar jaruma Fatima Yusuf wacce ake yi wa lakabi da Fatima Karmatako. Ta bayyana dalilan da suka sanya ta shiga harkar fim da kuma makasudin da ya sa ta jingine harkar na wucin-gadi.

 

Za mu so ki bayyana takaitaccen tarihinki?

Ni asalin iyayena ’yan garin Maiduguri ne da ke jihar Borno. Ni ce ’yar fari a gidanmu. Mahaifiyata da mahaifina duk kabilar Barebari ne. A garin Maiduguri aka haife ni amma a jihar Legas na tashi. Na yi karatuna na firamare da sakandire dina rabi a Maiduguri rabi kuma a Legas. Na yi difiloma a Maiduguri a fannin Addinin Musulunci. Daga nan kuma sai na tsunduma cikin harkar fim gadan-gadan babu kama hannun yaro.

Me ya sa kika shiga harkar fim?

Ni tun ina karama nake da sha’awar fim. Kuma abin ya samo asali ne daga kalle-kallen finafinan Indiya da nake yi. Finafinan Indiya suna ba ni sha’awa kuma suna burge ni har ta kai sai na rika tunanin cewa Indiyawa ba a duniyarmu suke ba. Saboda haka sai na rika sha’awar ni ma na kasance ina yin harkar fim. A yanzu na yi shekaru da yawa ina yin fim. Saboda haka babu abinda zan ce sai godiya ga Allah madaukakin sarki.

Za mu so mu ji finafinai nawa kika fito cikinsu?

Gaskiya ka san saboda kalubalen rayuwa ba zan iya kididdige finafinan da na fito a cikinsu ba amma dai wadanda zan iya tunawa su ne kamar fim dina na farko da ba zan taba mantawa da shi ba mai suna: “Muna son juna” wanda muka yi shi a jihar Kano wanda Nasiru ya yi daraktin din fim din. Akwai fim din “Nadama” shi ma ba zan taba mantawa da shi ba wanda Sadik M. Mafiya ya shirya da sauran wasu finafinai da na fito cikinsu masu yawa..

A cikin finafinan da kika yi wane fim ne ya fi kwanta miki a rai?

Gaskiya na fi son fim din “Nadama” na Sadik M. Mafiya, saboda matsayin da aka ba ni na matar aure. Ina mutukar tuna fim din saboda yadda aka shirya shi da kuma irin darussan da yake koyarwa. Sannan kuma sunan da aka baiwa fim din ya dace da shi, sannan kuma jarumai da masu taimaka musu da aka zabo sun taka rawar gani sosai. Shi kansa Sadik Mafiya ya yi mutukar kokari tare da yin zurfin tunani da hangen nesa. Sai fim din da ake kira “Muna son juna”. Shi ma fim ne da yake kayatar da ni saboda yadda aka shirya shi tare da darussan da yake koyarwa. Shi kuma na fito ne a kawar Amarya sannan kuma ina da wani saurayina Wada. Gaskiya shi ma fim ne da aka shirya shi don nishadantarwa da raha. Shi ma gaskiya fim ne wanda b azan taba mantawa da shi ba a cikin jerin finafinan da na fito cikinsu.

Wadanne nasarori za ki iya bayyanawa kin samu a harkar fim?

Gaskiya na samu nasarori da yawa. Wadanda suka hada da yin fice da yin suna tare da sanin jama’a. Kuma na mallaki kadarori masu yawa. Kuma gaskiya na gane masoyan na hakika da kuma makiyana daga cikin mutane. Saboda idan ka je wani wuri wanda ba ya son abin da ka yi a wani fim sai ya rika sukanka da shi kuma wanda yake son wani abu da ka yi shi kuma sai ya rika yabonka. Saboda haka a fili za ka gane mai sonka na gaskiya da wanda ba ya sonka.Babu nasorin da na samu ba za su kididdigu ba. Babu abin zan ce sai dai na yi wa Allah godiya da baiwar da ya yi mani a harkar fim.

Wadanne kalubale kika fuskanta?

Gaskiya na fuskanci kalubale masu yawa. Gaskiya saboda kalubalen da na fuskanta har sai da na bar industiri na fim na koma gefe na wani lokaci. Hakikanin gaskiya babban kalubalen da na fuskanta shi ne duk inda na je sai mutane su rika yi mani kallon karuwa ko ’yar iska wacce ba ta da mutunci da tarbiya, masu lalata ’ya’yan mutane, saboda fim din da muke yi. Wani zai tare ka ya gaya maka bakaken maganganu wani kuma zai rika nuna ka daga nesa. Saboda haka nake kira ga jama’a su daina yi wa ’yan fim kallon mutanen banza saboda matan da suke yin fim ba karuwai ba ne kuma ba ’yan iska ba ne. Mata ne wadanda suke da iyaye suke da mutunci kuma suke neman na kansu. Matan da suke yin fim ba ci-ma-zaune ba ne, ba kuma ragwaye ba ne. Mata ne masu hangen nesa, masu kishin kasa da al’ummarsu.

Idan kika tuna irin wadannan kalubale ya kike ji a ranki?

Gaskiya ina jin ba dadi amma kawai dai abin da na sani shi ne ina yin fim ne saboda Allah don in yi wa mutane wa’azi tare da isar da sako ga jama’a kan rayuwar duniya. Saboda haka idan na tuna haka sai in ji na samu sauki a raina.

Wane buri kike son ki cimma a harkar fim nan gaba?

Burina shi ne in fara yin fina-finai nawa na kaina wadanda jama’a za su gamsu da su kuma duk wanda ya kalla sai ya samu darasi. Amma yanzu na jinginar da harkar fim saboda wani aiki da nake yi wanda ba sai na baiyyana ba amma da yardar Allah zan ci gaba da yin fim ba tare da gajiyawa ba.

Me ya sa kika jingine harkar fim a yanzu?

Ba wai jingine harkar fim na yi kwata-kwata ba. Na jingine ta ne na dan wani lokaci. Fim shi ne zabina na farko a rayuwata saboda haka ba zan bar harkar ba.

Shin kina da sha’awar yin aure a yanzu?

Burin kowace ’ya mace ta yi aure a rayuwarta. Saboda haka wannan shi ne burina. Saboda haka ina bukatar addu’a daga masoyana don duk abin da kake so idan ba alheri ba ne a rayuwarka to ko da ka yi sai ka ga ba daidai ba. Ni kawai addu’a nake so Allah ya zaba mani mafi alheri.