Matan aure fiye da 40 ne suka yi zanga-zangar nuna adawa da karin lokacin aiki a ofisoshi, inda suka fito titin birnin Shangai na kasar Sin a ranar Litinin din da ta wuce. Zanga-zangar dai sun yi mata taken “ Kadaicin zaman kujera (The Lonely Sofa),” don nuna adawarsu ga karin sa’o’in aiki a ofis.
Wadanda suka fito zanga-zangar, matan aure ne da ke sanye da kayan barci farare, inda suka mike tsaye kan kujeru rike da kwalaye dauke da rubutun da cewa: “Kuna kaunata ko shugaban kuke so?” da kuma “Kun san cewa ina da juna biyu na tsawon mako hudu?”
Yin aiki na tsawon lokaci na illata lafiyar ma’aikatan kasar Sin. Yayin da aka tursasa wasu ma’aikata su shafe sa’o’i a kan tebur suna aiki, saboda matsin lambar abokan aiki ko ka’idar aiki, wasu kuwa na yin aikin ne cikin farin ciki.
Binciken da aka gudanar a shekarar 2015 a Jami’ar Sun Yat-sen, ya yi nuni da cewa kashi 60 cikin 100 na wadanda suka amince za su yi karin lokacin aikinsu cikin shekarar 2014, inda fiye da kashi 50 cikin 100 suke yin aikin don kudi ko “yin biyayya ga kamfaninsu.” Binciken an gudanar da shi ne a tsakanin fiye da ma’aikata dubu 23 da 590 da ke Larduna 29 a fadin kasar Sin.
Matan aure sun yi zanga-zangar adawa da karin lokacin aiki
Matan aure fiye da 40 ne suka yi zanga-zangar nuna adawa da karin lokacin aiki a ofisoshi, inda suka fito titin birnin Shangai na kasar…