Wasu mata a kasar Afghanistan sun shirya zanga-zanga a Kabul babban birnin kasar ranar Alhamis don nuna rashin amincewarsu da matakin gwamnatin Taliban na hana mata zuwa jami’o’i.
Matan sun kuma yi zargin cewa an kama wasu daga cikin su ’yan gwagwarmayar da suka jagoranci zanga-zangar.
- Ni zan jagoranci yi wa Tinubu kamfe a sabuwar shekara —Buhari
- Za a kafa dokar daurin shekara 5 ga masu yi wa mata kaciya
A ranar Talata ce dai Ma’aikatar Ilimi mai zurfi ta kasar ta sanar da daukar matakin hana matan zuwa dukkan jami’o’in gwamnati da masu zaman kansu da ke kasar.
Kamfanin Dillancin Labaran Faransa (AFP) ya rawaito daya daga cikin masu jawabi yayin zanga-zangar na cewa, “Sun kori mata daga jami’o’i. Ya ku mutane, ku kawo mana dauki. Ana kokarin tauye wa kowa hakkinsa.”
Ita ma wata mai zanga-zangar da ta nemi a sakaya sunanta ta shaida wa AFP din cewa wasu jami’an ’yan sanda mata sun kama wasu daga cikin matan. Ta ce an saki mutum biyu, amma har yanzu akwai wasu da dama da ke tsare.
Kusan mata 20 ne sanye da hijabi, wasun su kuma sanye da takunkumin rufe fuska suke ta daddaga hannuwa suna rera wakoki yayin da suke zanga-zangar a kan titunan Kabul.
Tun bayan karbar mulkin Taliban ake ta samun karuwar yawan zanga-zangar mata a kasar, a kokarinsu na yaki da wasu daga cikin manufofin gwamnatin kasar.
Sai dai duk wandanda aka kama da hannu a cikin zanga-zangar na cikin barazanar kamu ko fuskantar hukunci.
Da farko dai matan sun yi shirin taruwa a gaban Jami’ar birnin na Kabul, wacce ita ce babbar jami’a kuma mafi shahara a kasar, amma daga bisani suka canza waje bayan an girke jami’an tsaro a kofar shigar ta.
Sanarwar haramcin zuwa makarantun ga mata dai ta jawo suka daga kungiyoyin kasa da kasa, da kuma Majalisar Dinkin Duniya da Amurka da ma wasu kasashen Musulmai ke sukar lamirin Taliban kan matakin.