Wasu kungiyoyin jam’iyyar APC sun yi Allah-wadai da matakin Gwamnonin Arewacin Najeriya na mika takarar Shugabancin Kasa ga Kudancin kasar, suna masu cewa matakin zai iya kai jam’iyyar ga shan mummunan kaye.
Kungiyoyin wadanda suka bayyana matsayarsu a yayin wani taron ’yan jarida a daura da hedkwatar jam’iyyar ta kasa a Ranar Lahadi a Abuja, sun ce muradin Gwamnonin ya saba da kundin dokar jam’iyyar, wanda suka ce bai san da tsarin karba-karba ba.
Aminiya ta ba da labarin yadda Gwamnoni 10 a karkashin jam’iyyar daga shiyyar Arewa su ka bukaci Shugaban Kasa Muhammadu Buhari da ya fidda dan takara guda daga shiyyar Kudancin kasar nan don su mara masa baya a yayin zaven fid da gwani na jam’iyyar da zai fara a Ranar Litinin xin nan da ke tafe.
Sai dai a yayin korafin nasu, daya daga cikin jagororin kungiyoyin mai suna “APC Stakeholders forum”, Malam Abdullahi Aliyu Katsina, ya ce hakan tauye hakkin ’yan takara daga shiyyar Arewa ne wanda ya ce zai iya kai jam’iyyar ga shan kaye a yayin zabe na gama-gari.
“Daukacin Gwamnonin da ke neman wannan bukatar kowannensu shi kadai ne ya yi gaban kansa wajen zaba wa kansa magaji, amma sai ga shi Shugaban Kasa Buhari ya nemi shawararsu kan su taimaka masa a wajen zaba masa nashi magajin.
“Sai dai a maimakon su takaita abin a matakin ba da shawara, sai suka fitar da sanarwan cewa suna neman ya fid da dan takara daga yanki daya kadai.
“Wannan ba adalci ba ne, kuma ba zai haifa wa jam’iyyar APC da mai ido ba,” inji shi.
Haka ita ma daya kungiyar da ta bayyana korafin nata a yayin taron mai suna “Coalition of APC Support Group” ta ce tsarin karba-karba abu ne da tini a ka yi watsi da shi a matakin zaben Shugaban Kasa tun a lokacin zaben shekara ta 2015, inda ta ce ’yan takara daga daukacin yankunan Najeriaya suka nemi mukamin ba tare da hana ’yan wasu yanki ba.
Jagoran kungiyar ta kasa, Dokta Audu Alfred Gbaja wanda ya yi jawabi a madadin sauran shugabanninta, ya bukaci jam’iyyar ta APC da ta bar kuri’ar masu zaben ’yan takara na daliget, su yi aikinsu.
“Wannan ne kadai zai magance jawo baraka sannan ya bamu nasara kan dan takarar jam’iyyar adawa ta PDP,” a cewarsa.