Tsohon Kwamishinan ’yan sandan Jihar Kano, CP Muhammad Wakil mai ritaya wanda ake yi wa inkiyar Singham, ya ce matakin dakatar da DCP Abba Kyari da Hukumar ’yan sandan Najeriya ta yi izina ce ga sauran abokan aikinsa.
A zantawarsa da Sashen Hausa na BBC, Wakil ya ce matakin da aka dauka na kaddamar da bincike kan zargin da ake yi wa Kyari ya yi daidai domin hakan zai bayar da damar sanin gaskiyar lamarin kuma a yi wa kowane bangare adalci.
- Kungiyar Ci gaban Masarautar Doma ta karrama Gwamnan Gombe
- Mai taimaka wa IPOB da kudade daga kasar waje ya shiga hannu
A cewarsa, a yanzu babu ta cewa game da lamarin har sai abin da binciken Hukumar ya nuna, wanda daga nan ne za a san mataki na gaba da za a dauka a kansa.
Ya ce, “idan ta tabbata ya aikata laifin da ake zarginsa, za a yanke masa hukunci ne daidai da abin da ya aikata a bisa tanadin dokokin kasa da hukumar ’yan sanda,” a cewar Wakil.
A Lahadin da ta gabata ce Hukumar Kula da Aikin Dan sanda a Najeriya ta dakatar da Abba Kyari daga aikin dan sanda sakamakon zargin hannun a wata damfara da Hukumar Binciken Manyan Laifuka ta Amurka ta FBI ke yi masa.
Hukumar ta dauki matakin dakatar da Mataimakin Kwamishinan ’Yan sandan ne bayan shawarar da Babban Sufeton ’Yan sanda Usman Alkali Baba ya bayar.
Kyari dai ana zargin sa da karbar cin hanci daga hannun shahararren matashin dan Najeriyar nan da ke fuskantar tuhuma a Amurka kan ayyukan zamba na duniya, Abbas Ramon wanda aka fi sani da Hushpuppi.
Ana zargin Hushpuppi ne da zambatar manyan kafanoni da kungiyoyin kwallon kafa da kuma daidaikun mutane a kasashensu na fadin duniya.
Wasu bayanai da matashin ya fada wa masu bincike na cewa ya taba bai wa jami’in dan sanda Abba Kyari wasu kudade domin a daure wani abokin huldarsa, zargin da Kyari ya musanta.
Hukumar FBI ta bukaci hukumomin Najeriya da su binciki Abba Kyari bisa zargin karbar wasu kudade a matsayin cin hanci daga hannun Hushpuppi domin ya garkame masa wasu daga cikin abokanan huldarsa.