✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Matakin da za mu dauka bayan kotu ta sallami Nnamdi Kanu —Ministan Shari’a

Ministan Shari'a, Abubakar Malami, ya bayyana cewa kotu ba ta wanke Nnamdi Kanu daga zargin ta'addanci ba.

Ministan Shari’a, Abubakar Malami, ya bayyana cewa kotu ba ta wanke shugaban haramtacciyar kungiyar IPOB, Nnamdi Kanu, daga zarge-zargen ta’addanci ba.

Ministan ya ce Gwamnatin Tarayya na nazarin hukuncin kotun daukaka kara da ta sallami Kanu, duk da cewa yana fuskantar zargin ta’addnaci.

Malami ta Sanarwar da kakakinsa, Umar Jibrilu Gwanki ya fitar, ya ce, “Domin kawar da shakku, kotun da ta sallami Nnamdi Kanu ba ta wanke shi daga tuhuma ba.

“Saboda haka, hukumomin da suka dace za su bi matakan Shari’a da suka dace kan tuhumar, wandan nan gaba za a sanar da jama’a.

“Umarnin sallamar da kotun ta bayar a kan abu daya ne, wato dawo da shi Najeriya a asirce daga kasar waje.

“Jama’a su sani cewa sauran batutuwa da ake zargin sa a kansu gabanin tiso keyarsa zuwa Najeriya a asirce bayan ya tsallake beli na nan da ingancinsu, kotu za ta yanke hukunci a kai.”

Hakan kuwa na zuwa ne bayan lauyan shugaban na IPOB, Maxwell Okpara, ya ce wajibi ne Gwamnatin Tarayya ta saki Nnamdi Kanu a cikin kana 30 daga rana da kotun ta yanke hukuncin, idan har gwamnatin ba ta daukaka kara ba.

A cewarsa, bangarensu zai mika wa bangaren gwamnati takardar hukuncin domin yin abin da ya dace, na sakin wanda yake karewa ko kuma daukaka kara.

Sai dai Ministan Shari’a, Abubakar Malami, ya ce, “Gwamnati za ta yi amfani da duk damar da doka ta bayar game da umarni wannan kotu na sakinsa kan yadda aka dawo da shi (Nnamdi Kanu) zuwa Najeriya.

“Haka kuma gwamnati za ta ci gaba da neman hukuncin kan tuhume-tuhumen da ake masa gabanin kamo shin.”

A ranar Alhamis ne Kotun Daukaka Kara ta Tarayya da ke Abuja ta yi watsi da zargin Kanu da ta’addanci, bisa hujjar cewa gwamnati ta sato shi ne daga kasar Kenya domin gurfanar da shi.

A hukuncin kotun, Mai Shari’a Hanatu  Sankey, ta ce alkalan guda uku sun yi ittifakin cewa tun da gwamanti ta kasa amsa tambayoyin bangaren da ake zargin, to ta amince cewa da karfin tuwo ta dawo da shi Najeriya daga kasar Kenya.

Hukuncin da Mai Sharia’ Adedotun Adefope-Okijie ya karanta, ya ce, yana da muhimmanci gwamnati ta gabatar wa kotun hujjoji da ke nuna ta halastacciyar hanya aka dawo da Nnamdi Kanu Najeriya.

Kotun ta ce gwamnati ta saba Dokar Yaki da Ta’addanci da sauran dokokin kasa da kasa game da daukko mai laifi daga wata kasa, kuma ta tauye hakkin wanda ake zargin.

Don haka alkalan suka ce kasacewar ta haramtacciyar aka dawo da wanda ake zargin daga kasar waje, kotun ba ta da hurumin ci gaba da gurfanar da Nnamdi Kanu.

Kotun ta ce abin da gwamnati ta yi ya dagula shari’ar da take karar Kanu, kuma abin da ta yi, “wuje haddi ne a tsarin gurfanar da manyan laifuka”.

“Kotu ba za ta daina kira ga bangaren zartarwa ba a duk lokacin ta bangaren ya wuce gona da iri”, in ji sanarwar hukuncin kotun.

Don haka kotun ta amince da bukatar Kanu na sallamar sa.

%d bloggers like this: