✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Matakan lura da ciki bayan haihuwa

Assalamu alaikum, barkanmu da sake saduwa cikin wannan filin. A wannan makon zan yi wa mata bayani ne kan yadda za su lura da cikinsu…

Assalamu alaikum, barkanmu da sake saduwa cikin wannan filin. A wannan makon zan yi wa mata bayani ne kan yadda za su lura da cikinsu bayan haihuwa. Allah Ya sa bayanin ya amfanar da masu bukatarsa, amin.

Sau da dama nakanji matan da suka haihu na korafin cikinsu ya ki sabewa ko komawa yadda yake kafin su haihuwa. Girman cikin na sanya kasa gane ko wadansu sun haihu ko har yanzu suna da ciki.
Wadannan mata ba sa bin matakan da ya kamata su bi wajen lura da cikinsu. Idan kun haihu akwai abubuwan da ya kamata ku rika yi wadanda suka kunshi motsa jiki da cin ’ya’yan itatuwa da sauransu.
Likitoci sun ce ya kamata ku fara motsa jiki makonni 6 zuwa 8 bayan haihuwa, kodayake wadansu yakan fi hakan, ga wadanda aka yi musu tiyata kuma ya danganta zuwa lokacin da suka ji sun samu lafiya.
Sannan yana da kyawu kafin a fara motsa jikin a nemi shawarar likitoci. Idan cikin ya ba ku matsala kafin ku haihu ko kuma an yi muku tiyata, yana da kyawu ku fara da mimmike jikinku, daga nan ku rika yin sauran nau’ikan motsa jiki.
Motsa jiki na ciki
Ciki shi ne abu mafi muhimmanci a gare ku, kuma shi ne kuke so ya koma yadda yake kafin haihuwarku, don haka motsa jiki na zama da ake kira ‘sit-ups’ za ku rika yi, domin hakan zai sanya cikinku ya koma kamar yadda yake kafin ku haihu cikin sauri.
A lokacin da kuka fara motsa jikinku akwai karfi sosai a tare da ku, don haka za ku motsa jikinku sosai tsawon mako biyu, hakan zai sanya jijiyoyi da naman cikinku ya fara komawa kamar yadda yake kafin ku haihu. Yayin da kike motsa jikin ‘sit-ups’ ku tabbata kuna yin sa a kan taburma, wani lokaci kuma ku rika kwantar da bayanku a kan dandamalin sumunti.
Don motsa jijiyoyin cikinku na sama, sai ku kwanta a bayanku, sannan ku lankwasar da gwiwowinku, sannan ku tabbata tafin kafafunku na taba dandamalin sumunti ko taburmar da kuke motsa jikin a kanta. Za ku iya dora tafin kafafunki a kan kujera, don su ba da kusurwa 90. Daga nan ku dora hannuwanki a bayan kanku, sannan ku shaki iska, ku daga kanku da kafadunku sama, sannan ku yi kokarin tashi, daga nan ku dame jijiyoyi da naman cikinku. Za ku ci gaba da tashi har sai kun tabbata jijiyoyin cikinku sun mike, sannan ku rika komawa a hankali, sannan ku sake iska.
Don motsa jijiyoyin cikinku na kasa kuma, maimakon ku dame cikinku sai ku rika hura shi, sannan ku rika sacewa.  Za ku yi hakan kamar sau 10 zuwa 12.
Za mu ci gaba in sha Allahu.