Hukumar yaƙi da masu yi wa tattalin arzikin ƙasa zangon ƙasa a Najeriya (EFCC), ta koka kan yadda take yawan samun rahotanni na waɗanda aka cire wa kuɗi daga banki ba tare da saninsu ba kuma akasari ta ATM.
Hukumar ta ce akasarin ’yan damfarar sun fi samun bayanan jama’a ko katin ATM ɗin mutane a wuraren cirar kuɗi na ATM ko kuma masu POS.
- Tinubu zai tafi Dubai taron sauyin yanayi ranar Laraba
- Tinubu zai ranto bashin dala biliyan daya a Bankin Raya Kasashen Afirka
EFCC ta yi gargadi kan cewa ’yan damfarar suna amfani da katin ATM na bankin mutumin da suke so su yaudara, bayan haka sukan je wurinsa da niyyar taimako idan ya shiga ruɗani a gaban ATM.
Hukumar kamar yadda TRT ta ruwaito, EFCC ta ce ’yan damfarar kan yi sauri su yi wa kwastoman bankin musaya da katinsa bayan su haddace lambobin sirrinsa a lokacin da suke ƙoƙarin taimakonsa, wanda daga baya sai su cire kuɗin da ke asusun ajiyarsa.
Dangane da haka ne hukumar ta fitar da hanyoyi takwas waɗanda take ganin idan jama’a sun bi su za su samu kariya daga masu damfarar:
1. Akwai buƙatar ajiye kati a amintaccen wuri. Duk lokacin da ka karɓi katinka bayan cire kuɗi, ka tabbata katinka ka karɓa ba wai wanda ke kama da katinka ba.
2. A rinƙa duba sauran kuɗin da ke asusu (balance) domin dubawa ko an cire kuɗi daga asusu.
3. Saka ƙararrawa domin lura da duk wani abu da ya shafi asusun ajiya ko katin banki.
4. Rufe lambobin da ake latsawa a jikin ATM ko POS da hannu a lokacin da ake saka lamobin sirri domin cire kuɗ i ko wani amfani.
5. A rinƙa neman taimako daga jami’an banki, ka da ka yi saurin biyan kudi ko cire kuɗi.
6. A kira banki domin toshe katin ATM a duk lokacin da aka lura kati ya maƙale a cikin ATM ko kuma duk lokacin da aka lura da wani lamari wanda yake ba daidai ba.
7. A tabbata an san lambar da za a iya toshe ATM da ita tare da amfani da ita cikin gaggawa a duk lokacin da aka ɓatar da katin ko aka sace shi.
8. A latsa lambobin USSD na *966*911# da kuma bin matakan da suka biyo baya domin toshe katin ATM nan take.