✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Mataimakiyar Shugaban Amurka ta kamu da COVID-19

Fadar White House ta ce kamuwar tata ba ta da alaka da kusanci da Shugaba Joe Biden

Rahotanni daga Kasar Amurka na nuni da cewa, Mataimakiyar Shugaban Kasar, Kamala Harris, ta kamu da cutar COVID-19.

Fadar White House ta ce kamuwar tata ba ta da alaka da kusanci da Shugaba Joe Biden ko kuma mai dakinsa.

A cewar Sakataren Yada Labarai ga Harris, Kirsten Allen, “A yau, gwajin da aka yi mata ya nuna Mataimakiyar Shugaban Ƙasa Harris na dauke da kwayar cutar Korona. Don haka za a killace ta sannan ta ci gaba da aiki daga gida.

“Ba ta zamo tana kusantar shugaban kasa ko mai dakinsa ba saboda yanayi na tafiye-tafiye,” in ji Allen.

Ya kara da cewa, Harris za ta koma Fadar White House bayan an tabbatar da ta rabu da kwayar cutar a nan gaba.

Da wannan, Harris ta zama wadda aka samu dauke da kwayar cutar Korona a baya-bayan nan daga fitattun ’yan Kasar Amurka.

Duk da dai magidanta ya harbu da cutar a watan Maris, amma hakan bai sa Harris ta kamu da cutar ba sai a wannan karon.

A farkon wannan watan ne aka ji Daraktan Sadarwa na Fadar White House na cewa, “Mai yiwuwa shi ma Shugaba Biden ya harbu da kwayar cutar, duk da dai an yi masa rigakafin kariya daga kamuwa da ita.”

Kawo yanzu, sama da mutum 900,000 ne Korona ta kashe a fadin Amurka inda a halin da ake ciki takan hallaka kimanin mutum 300 a duk yini.