✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mataimakin Kakakin majalisar Abiya ya sha kaye

Mataimakin kakakin majalisar dokokin jihar Abiya Rt. Hon. Dakta Cosmos Ndukwe  dan takarar jam’iyyar PDP ya sha kaye a takarar dan majalisar dokokin jihar da…

Mataimakin kakakin majalisar dokokin jihar Abiya Rt. Hon. Dakta Cosmos Ndukwe  dan takarar jam’iyyar PDP ya sha kaye a takarar dan majalisar dokokin jihar da yake nema karo na biyu.

Dan takarar majalisar dokokin jihar na jam’iyyar APC  Chijioke Chukwu ne ya yi nasara a mazabar Bende ta Arewa.

Sakamakon zaben da aka kada na bayyana cewa, Jam’iyyar APC nada kuri’u 12,172, PDP nada 7,265 yayin da APGA keda kuri’u 4,238.