Wani harin bam da wasu mahara suka dasa a jikin mota a Afghanistan ya yi sanadiyyar mutuwar mataimakin gwamnan birnin Kabul, Mahboobullah Mohebi.
Ma’aikatar Al’amuran Cikin Gida ta Kasar ta ce mataimakin gwamnan ya gamu da ajalin sa ne lokacin da wasu da ba a san ko su wane ne ba suka dasa wa motar sa wani bam da ya tarwatse, yana kan hanyar sa ta zuwa wurin aiki a ranar Talata.
- Harin Bam ya kashe jami’an tsaro 30 a Afghanistan
- Harin bam: Mataimakin Shugaban Kasar Afghanistan ya sha da kyar
Wata kafar watsa labarai a kasar ta rawaito ’yan sanda na cewa Mahboobullah da sakataren sa sun mutu ne sakamakon wani abin fashewa da aka makala a jikin motar da suke kai.
Har yanzu dai babu wanda ya dauki alhakin kai harin wanda a cikin sa karin masu tsaron lafiyar sa mutum biyu su ma suka jikkata.
An yi ta samun tashin-tashina a fadin kasar tun bayan da gwamnatin kasar da kungiyar Taliban suka kaddamar da tattaunawar zaman lafiya a kasar Qatar a watan Satumba.
Kasar, musamman kuma birnin Kabul sun yi ta fama da kashe-kashen manyan mutane ciki har da ’yan jarida, malaman addini, ’yan siyasa da ’yan gwagwarmaya.
Ko a makon da ya gabata sai da aka harbe wata ’yar jarida har lahira a birnin Jalalabad, ’yar jarida ta biyu kenan da aka kashe cikin kasa da wata daya.
Kazalika, birnin na Kabul ya fuskanci harin rokoki har sau biyu a wannan watan a kan makarantu, wanda ya janyo asarar rayukan daliban jami’a da dama.
Ana sa ran bangarorin biyu su dawo teburin tattaunawar da aka yi watsi da ita tun a watan Janairu a cikin makon nan a kasar Qatar.