Rundunar Sojin Najeriya ta damke mataimakin Terwase Akwaza, wanda aka fi sanda da Gana, babban dan ta’addan jihar Binuwai da sojoji suka bindige a kwanakin baya.
Kwamadan Rundunar ta Musamman da ke Doma, Jihar Nasarawa, Manjo Janar Ali Mounde ya gabatar da Kumaor Fachii a gaban ’yan jarida.
“Mun damke Fachii ne a Karamar Hukumar Katsina Ala, Jihar Binuwai a lokacin da yake tare da budurwarsa.
“Gana da ’yan kungiyarsa sun tayar ad hankalin jama’a a Jihar Binuwai da makwabtanta a shekaru biyar da suka wuce.
“Bayan mutuwarsa an yi ta hasashen cewa ya mika shugabancin kungiyar ga mataimakinsa, Kumaor Fachii”, inji shi.
Da yake amsa tambayoyin ’yan jarida a ofishin rundunar, Fachii ya ce, “Ni dan kungiyar Gana ne amma ba ni ba ne mataimakinsa”.
A watan Satumba ne sojoji suka bindige Terwase Gana bayan sun kama shi a hanyar zuwa Makurdi tare da wasu yaransa inda gwamantin jihar ta ce za su je ne domin karbar afuwa.
Sai dai ko a lokacin, sojoji sun ce sun kashe shi ne a musayar wuta da suka yi a lokacin da suka kama shi.