✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Matafiya 8 sun kone kurmus a hanyar Legas

Mutum takwas aka sanar sun yi gamo da ajali a kan babbar hanyar Legas daga Ibadan bayan da motarsu ta kama da wuta. Matafiyan na…

Mutum takwas aka sanar sun yi gamo da ajali a kan babbar hanyar Legas daga Ibadan bayan da motarsu ta kama da wuta.

Matafiyan na kan hanyarsu a cikin motar bus a ranar Asabar 19 ga watan Satumba, bayan da tayar motarsu ta fashe, da hakan ya sa ta kwace wa direban ta kuma kama da wuta.

Kwamandan Hukumar Kiyaye Hadura ta kasa (FRSC) mai kula da shiyyar Ogun, Ahmed Umar ya shaida wa Aminiya cewa mutum 11 ne a cikin motar kirar Mazda mai lamba AAA 249 VX.

Ya ce Jami’an Hukumar da ke aiki a yankin Shagamu sun ankarar da jami’an hukumar kashe gobara yayin da mummunan tsautsayin ya auku.

“Mun yi nasarar ceto mutum uku da ransu wadanda aka garzaya da su asibitin Idara da ke Shagamu domin ba su agaji, yayin da aka kai gawarwakin wadanda suka kone cibiyar lafiya ta Karamar Hukumar Remo da ke jihar Ogun.”

Ahmed Umar ya yi kira ga direbobin motoci da su rika tuki cikin nutsuwa tare da bin doka da ka’idojin hanya.