Wata matar aure da ta yi garkuwa da mijinta ta karbi kudin fansa ta shiga hannun hukuma.
Dubun matar ta cika ne bayan sun karbi kudin fansa Naira miliyan biyu bayan ta yi garkuwa da mijin nata.
- An kama fasto ya yi wa ’yar shekara 12 fyade a coci
- ’Yan bindiga sun yi garkuwa da mutane a masallacin Juma’a a Zamfara
Sai dai ta shaida wa ’yan sanda cewa, “Wanda ya yi garkuwa da shi ya karbi kudin fansa Naira miliyan biyu, amma bai ba ni kasona daga ciki ba, ko kamannin kudin ban gani ba.”
Ta bayyana cewa ta sa an yi garkuwa da shi ne saboda rashin kwanciyar aure da ita da kuma watsi da ’ya’yansu.
Matar dai tana cikin mutum 29 da ’yan sanda suka gabatar wa ’yan jarida kan zargin garkuwa da mutane da sauran laifuka aa Jihar Akwa Ibom.
A cewarta, sakamakon watsi da ita da maigidanta ya yi ta fara yin aikatau domin ciyar da kanta da ’ya’yansu bayan mijin ya auri wata mata.
Hakan ne, a cewarta ya tilasta ta kitsa sace shi domin ta samu kudin kula da kanta da ’ya’yanta daga hannunsa, amma ta yi rashin sa’a asirinsu ya tonu ba tare da an ba ta rabonta daga cikin kudin ba.
Magidancin da aka kubutar, ya ce tun ranar 21 ga watan Yuli, 2022 aka yi garkuwa da shi a harabar gidansa.
Da yake jawabi, Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Akwa Ibom, Olatoye Durosinmi, ya ce rundunar ba za ta yi kasa a gwiwa ba, wajen murkushe ayyukan laifi a fadin jihar.