Wata kotu a unugwar Mapo a garin Ibadan, Jihar Oyo ta raba auren da ya shekara takwas tsakanin Bushirat Adeoko da mijinta Olamiji wanda ta gano ya ajiye daduro.
Bushirat ta yi karar mijin nata ne a gaban kotu bisa zargin ya ajiye farkar da ta haifa masa ’ya ba da saninta ba.
- Kotu ta raba auren shekaru 12 saboda saurin fushin mata
- Ya gurfanar da matarsa a gaban kotu bisa zargin yunkurin kashe shi
- Tsaftar Muhalli: Kotu ta rufe tashar mota da gidan mai a Kano
- Magidanci ya caka wa matarsa wuka a kotu a Kano
“Yana da ’ya mai shekara takwas da aka haifa ba ta hanyar aure ba; ni ma ban taba sani ba sai bayan na haihu.
“Ya guje mu ni da dana wata 10 da suka wuce,” kamar yadda ta bayyana wa kotun.
Alkalin kotun, Ademola Odunade, yayin da yake yanke hukunci, ya ce tunda babu yarda da amana a tsakanin ma’auratan, rabuwarsu ita ce mafi dacewa.
Alkalin ya umarci matar ta ci gaba da rainon danta, shi kuma tsohon mijin nata ya rika ba da N5000 kudin raino a duk wata.
Har wa yau, kotun ta umarci Olamiji ya dauki nauyin karatu dan nasa.
Olamiji, ya amsa laifukan da ake tuhumarsa da su a gaban kotun, sai dai ya ce damwarsa ita ce matar ba za ta iya kula da yaron ba yadda ya kamata.