✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mata sun fara wasan kwallon kafa a Somaliya

Rahotanin da ke fitowa daga Somaliya sun ce wadansu mata a kasar sun bijire wa dokar da ta hana su yin shagali da kuma wasanni…

Rahotanin da ke fitowa daga Somaliya sun ce wadansu mata a kasar sun bijire wa dokar da ta hana su yin shagali da kuma wasanni ciki har da buga kwallon kafa, inda aka ga wadansu daga cikinsu suna yin atisaye a wani filin kwallo kafin su shiga murza leda.

Sai dai a yayin da matan suke atisayen, an ce jami’an sojoji ne ke kewaye da su a wani filin wasa da ke Mogadishu babban birnin kasar don gudun kai musu hari.

Laifi ne babba a Somaliya a ga mata suna bikin sharholiya ko yin wasannin da suka hada da wasan kwallon kafa.

Kamar yadda rahoton ya nuna, matan sun bijire wa wannan doka ta Al-Shabab wacce ke mulkin kasar wajen yin wasan kwallon kafa.

A zantawar da aka yi da wadansu daga cikin matan sun ce a gaskiya sun gaji da zaman dirshan da hana su yin walwala musamman a al’amurran da ba za su saba wa dokar Musulunci ba.

Sai dai zuwa hada wannan rahoto gwamnatin kasar ba ta fitar da wani bayani game da bijirewar matan wajen buga kwallon kafa ba.