Assalamu alaikum, barkanmu da sake saduwa cikin wannan fili mai albarka. Muna fata kuna cikin koshin lafiya. Ga ci gaban labarin da muke kawo muku makonni 7 da suka gabata. Muna fata kuna daukar darussan da suke kunshe cikin labarin. A sha karatu lafiya:
karar da wayata ta fara yi ne ya sanya Halima ta yi shiru, na duba wayar sai na ga bakuwar lamba ce, bayan wayar ta kaste ne na sanyata a ‘silent’, inda ta gyara zama, sannan ta ci gaba da ba ni labari, inda ni kuma na kara tattara hankalina gare ta:
“A ranar da Mufeeda ta zo wurina murna gare ni ba a magana, domin bakina har kunne tsabar farin ciki, na shirya muka fita, inda ta bukaci in nuna mata daya daga cikin manya shagunan sayar da magunguna a Jos, ban bata lokaci ba wajen kai ta daya daga ciki, cikin salo na wayo ta nemi kebewa da daya daga cikin masu sayar da magungunan, bayan sun kebe ne na bi su, ta yi masa bayanin irin magungunan da muke so, maganguna ne masu sa maye da kuma barci. Ta yi ciniki da shi, sannan ta ce zan rika zuwa ina samunsa don ya samar mini da wasu idan wadanda ya ba ni suka kare. Bayan ta kalle ni ne, ta bukaci in ba shi kudin, na ciro kudi a cikin jakata na ba shi, sannan ta bukaci in ba shi wani kudin kyauta, nan ma na cire na ba shi.
A kan hanyarmu ta dawowa ne, take sanar da ni in rike shi sosai, zai rika samar mini duk abin da nake so. Mun kusa isa gida ne ta shiga yi mini kwakwazo: “Da ma na fada miki babu wani abu a cikin aure face bacin rai da bakin ciki, kin gan ni babu abin da ya dame ni, sai dai in wanke goma in tsoma biyar, in yafici duniya da tsinke, kudi a gida, kudi a mota, kudi a banki, babu wani namiji da zai daga mini hankali, babu wata mace wai kishiya da za a ce ta shiga hancina da kudundune, babu wadansu kannen miji ko ‘yan uwan miji da za su rika sanya ni zubar da hawaye. In fita daga gida lokacin da nake so, in koma lokacin da nake so, in kuma yi tafiye-tafiyena lokacin da nake so. Na dai yi shiru ina jinta. Ganin na yi shiru ina kallonta, sai ta ce mini “Kawai idan kin ga wannan aure zai zame miki alakakai to jefar da shi a bola mu ci gaba da harkarmu, tun da kin ga babu wani abu na kyawunki da ya bata, idan ma ya bata za mu je kanti mu dawo da shi. Na yi dariya, ita ma ta yi dariya”
Mufeeda ta yi shiru a lokacin da take kokarin kauce wa wani dan acaba, hakan shi ya sa na fara magana: “Abin da ba ki gane ba shi ne, matsalar rashin haihuwa ba wata aba ba. Ta yi dariya, “idan kuwa haka ne wadannan magungunan za su kawar miki da damuwarki.” Inji ta.
Haka dai ta ci gaba da tuki tana kuma kokarin ganin in kashe aurena in fito don mu ci gaba da harka, amma tasirin son Yasir ya hana ni aikata hakan.
A ranar farko da na sha maganin na kwana, na kuma wuni ina barci, duk wata damuwar da ke raina na ji babu ita, domin a lokutan baya yadda na ga rana haka nake ganin dare, duniyata ta fitinu da damuwar rashin haihuwa, duniyata ta kidimu da cin mutuncin surukata da dangogin mijina, amma magungunan sai suka dauke hankalina, suka bugar da ni har ya kasance ba na cikin hayyacina ballantana in samu natsuwar yin cikakken tunani. Sai dai hakan ya haifar mini da matsala a wurin mijina, domin ya fahimci sabuwar rayuwar da na fada, inda hakan ya bakanta masa rai, har ya kasance yana neman kaurace mini.
“Wata rana da ya same ni a cikin hayyacina ya rika shiga yana fita wajen yi mini fada, na san ba ni da gaskiya don haka ban tanka masa ba, a karshe ma hakuri na ba shi, na nuna masa rashin haihuwa da kuma yadda ‘yan uwansa suke yi mini ummul’aba’isin fadawata cikin wannan halin. Ya kwantar mini da hankali, ya nuna mini Allah (SWT) na jarrabar bawansa ta kowane hali, amma idan bawa ya kasance mai hakuri da juriya sai ya ci jarrabawar, inda a karshe duniyarsa ta dawo sabuwa. A lokacin ban dauki zancensa da muhimmanci ba, domin magungunan sun shiga raina, sun taka muhimmiyar rawa wajen bugar da ni har in manta da duk wata damuwa da ta addabi duniyata. Bayan ya yi fadansa ya fita ne, maimakon in shiga taitayina sai na debo magungunana na shanye.
Za mu ci gaba.
Za a iya samun Bashir Liman a wannan lambar 07036925654.