Maiduguri, G.R.A/Babban Falo
“Har Mufeeda ta yi fakin a cikin wani makeken gida zuciya ba ta daina tunanin daular da na gani a gidan ba. Bayan ta buDe motar ne muka fito, sannan sannu a hankali muka nufi kofar shiga wani kayataccen falo na gani na faDa, inda tun daga nesa za ka jiyo karar sautin kiDan da ke tashi a cikinsa. Bayan ta kalle ni ne ta yi murmushi, na yi mata murmushi. “Kada ki manta huDubar da na yi miki fa? Za ki samu masoya yau. Ina so ki ja zarenki daidai, kada ki yarda ya tsinke.” Na gyaDa mata kai, sannan muka shiga ciki.”
“Muna shiga cikin falon hankalin mutanen da ke ciki ya dawo kanmu. Na tafiyar da ganina cikin falon. Abin da na gani ya ba ni mamaki, domin yawancin mazajen da suke falon sun haife ni, amma ga zankaDa-zankaDan ‘yan mata cikin shigar matsattsun kaya na kaiwa da komowa a falon. Falon Dauke da kujerun alfarma. Kowace kujera akwai teburi a gabanta, teburan na Dauke da kayan ciye-ciye da lashe-lashe da kuma shaye-shaye. A cikin falon akwai manya-manyan lasifikoki uku, inda sauti ke fitowa daga cikinsu.”
“Bayan na kalli Mufeeda ne na ga ta fara hange-hange, can fuskarta ta washe bayan ta hango wani dattijo sanye da farar T-shirt da bakin jeans, kansa suwal-suwal sai kyalli yake.Ta kama hannuna sannan muka karasa wurinsa, ganinta ya sanya ya yi murmushi, ya mike tsaye, sannan suka rungumi juna. Na ci gaba da kallonsu. Ta gabatar da ni a wurinsa, sannan nima ta gabatar masa da ni. Hamshakin mai kuDi ne a Jihar Barno. Ta kwanta a jikinsa tana yi masa kwarkwasa da shagwaba, daga bisani ta rika shafa tumbinsa. Ya lumshe idanu, daga nan ta zuba ruwan jus a cikin wani kofin gilashi ta ba shi a baki. Haka ta ci gaba da sarrafa shi kamar jariri, yayin da ni kuma na ci gaba da kallonta, lokaci zuwa lokaci takan kibta mini ido, haDe da yin murmushi.”
“Ana cikin haka ne sai wani dattijo da ke daidai tsakiyar falon ya fara magana, sanye yake da bakar T-Shirt da bakin wandon jeans, “Kamar yadda kuka sani mun taru ne domin mu taya Hafsat ‘yar lelena murnar zagayowar ranar haihuwarta.” Ganin Hafsat ta nufo inda yake ne, sai ya yi shiru, mu kuma muka ci gaba da kallonta. Bayan ta tsaya a gefensa, daga nan ya ci gaba da jawabi. “Muna rokon Allah Ya albarkaci rayuwarki, ya sa ki yi tsawon kwana don mu ci gaba da cin gajiyarki…” Dariyar da jama’a suka barke ne ta sanya ya yi shiru. “Ko ba haka ba? Kun ga laifina?” Ya tambaya. “A’a.” Aka amsa masa, sannan aka sake kwashewa da dariya. Ya ci gaba da magana:
“Sakamakon wannan muhimmiyar rana ce a wurina, don haka nake sanar da jama’a cewa na ba babyna Hafsat kyautar mota, zan kuma Dauki nauyinta zuwa Landan don ta yi mako biyu tana shakatawa.” Falon ya Dauki kara sakamakon tafin da muke yi. Hafsat ta yi tsallen murna, sannan ta sumbace shi a kumatu. Bayan ya kammala jawabi ne aka yanka ket, Hafsat ta yi jawabin godiya, sannan aka shiga harkar rakashewa.”
Muna cikin rawa ke nan, sai wani Alhaji ya matso kusa da Mufeeda, sannan ya faDa mata cewa yana sona. Ta raDa mini a kunne, na kalle shi, sai na basar. Daga nan ta kama hannuna muka kebe gefe guda.
Bayan ta dafa kafaData sai ta fara magana: “Arziki ya zo miki, domin hamshakin mai kuDi ne, mata da yawa sun nemi ya yi tarayya da su amma ya ki, kakarki ta yanke saka. Za ki more shi, za kuma ki kasance cikin sahun manyan mata a kasar nan. Ke dai ki bi shi a hankali.” Na yi mata dariya, domin na daDe ina fatan samun mutum mai kuDi sai ga shi tsuntsu daga sama gasasshe, tsuntsun da namansa ya kasance guba a gare ni. “Ki bari kawai, kin san ba zan ba ki kunya ba.” Na ba ta amsa ganin ta zuba mini ido don jin me zan ce da ita. Bayan ta daki bayana, “Shegiya, na san ki ke ma ba tayar baya ba ce.” Cikin dariya muka koma cikin falon, mun same shi zaune a Daya daga cikin kujerun da ke falon, ya yi shiru kamar mutumin da ya kamu da ciwon damuwa. Ganinmu ne ya sanya ya Dan sake jikinsa, na zauna a kusa da shi, Mufeeda na kusa da ni, daga nan na kashe masa ido, ya yi dariya.
“Na san ba za ki ba ni kunya ba, na kamu da sonki, so na gaskiya ba wai don kawai mu huta ba.” Na kalle shi, sannan na kalli Mufeeda, ta tabe baki. “Ka ce son kawata ya harbi zuciyarka?” Ta tambaye shi. Ya yi dariya, “Kamar yadda wuka mai zafi take yanka biredi mai laushi ba.” Ya ba Mufeeda amsa. Muka sake yin dariya, abin mamaki sai na ji kai-tsaye ya kama hannuna. Na duba don in ga ko akwai mai kallonmu, sai na ga kowa sha’anin gabansa yake yi, wani dattijo kam ma ya rungume wata budurwa sai gurnani yake kamar mahaukaciyar zakanyar da ta shafe mako ba ta ci abinci ba. Na kalli Mufeeda ta yi mini alamar in bararraje. Ganin na yi masa wani irin kallo ne sai ya jawo ni jikinsa.
Za mu ci gaba.
Mata da shaye-shaye: Labarin Halimar Jos (5)
Maiduguri, G.R.A/Babban Falo“Har Mufeeda ta yi fakin a cikin wani makeken gida zuciya ba ta daina tunanin daular da na gani a gidan ba. Bayan…