An gurfanar da wasu ma’aurata a gaban Kotun Majistare ta Jihar Osun da ke zamanta a birnin Oshogbo bisa zargin datse sassan jikin wata gawa.
Dan sanda mai shigar da kara, John Idoko ya ce an fara gurfanar da ma’auratan ne a watan Maris, 2020 bisa zargin cire kai da kuma hannun gawar.
- Kotu ta yanke wa matashin da ya daddatse matar aure hukuncin kisa a Jigawa
- Za mu biya ma’aurata Dala 3,000 su jaraba katifarmu
Sai dai a sabuwar tuhumar da aka karanta musu ranar Juma’a, an zarge su da hada baki wajen aikata rashin imanin ga gawar a garin Dagbolu dake yankin Ifon a jihar ta Osun.
Takardar tuhumar dai ta yi zargin cewa, “A ranar 21 ga watan Maris 2020, mutane biyun da ake tuhuma da ma karin wasu sun hada baki ta hanyar datse kai da kuma hannun gawar wani mutum mai suna Rasheed Tiamiyu”.
Laifukan a cewar dan sandan sun saba da sashe na 242 na Kundin Manyan Laifuffuka na Jihar Osun na 2002.
Sai dai wadanda ake zargin sun musanta aikata laifin.
Lauyansu, Yemisi Akintajuwa ya roki kotun da ta bayar da belin su domin su shaki iskar ’yanci kamar yadda a baya kotun ta amince.
Alkalin kotun, Mai Shari’a Olusegun Ayilara ya amince ya bayar da su belin tare da dage ci gaba da sauraron karar zuwa ranar 8 ga watan Janairun 2021.