Wasu masu zanga-zangar neman Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya sauka daga kan mulki wato ‘Buhari Must Go’ sun fara kone-kone a kan titin Umaru Musa ’Yar’adua dake Abuja a ranar Litinin.
Hanyar dai ita ce take zuwa har filin jirgin sama na Nnamdi Azikiwe da ke Abujan.
- Satar dalibai na barazana ga ilimi a Arewa – Ahmed Lawan
- SSS ta kama mawaki a Kano kan wakar batanci
Lamarin dai ya kawo tarnaki ga masu ababen hawan da ke kokarin wucewa ta kan babbar hanyar.
Masu zanga-zangar dai sun rika rera wakokin ‘Dole Buhari ya sauka’ da kuma daukar kwalaye masu dauke da rubuce-rubuce iri-iri.
Hakan ya tilasta wa masu ababen hawa tafiya a hankali saboda kaucewa wutar da aka kunna a tsakiyar titi.
Ko a rabar 12 ga watan Yunin 2021 sai da aka gudanar da makamanciyar irin wannan zanga-zangar a Abuja, amma daga bisani an kama kusan dukkan masu hannu a cikinta.
Daga bisani, jagoran masu fafutukar #RevolutionNow, Omoyele Sowore ya saka hotuna da bidiyon masu zanga-zangar a shafukan sada zumunta.