✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Masu zanga-zangar EndSARS sun rufe hanyar Bwari-Kaduna

Masu zanga-zangar #EndSARS sun sake komawa yankin Dutsen-Alhaji da ke kan hanyar zuwa garin Bwari Abuja, inda suka datse shataletalen da aka fi sani da…

Masu zanga-zangar #EndSARS sun sake komawa yankin Dutsen-Alhaji da ke kan hanyar zuwa garin Bwari Abuja, inda suka datse shataletalen da aka fi sani da suna Saukale junction, a safiyar Litinin.

Hanyar ita ce mafita ga masu zuwa Kaduna a baya-bayan nan inda ake ratsawa ta garin Jere, saboda kaurace wa babbar hanyar Abuja zuwa Kaduna da wasu matafiya ke yi.

Tun kafin karfe 10 na safiyar Litinin, masu zanga-zangar suka tare hanyar, wadda kuma ta sada garin Kubwa da Abuja, lamarin da ya hana kaiwa ko tahowa daga kwariyar birnin ta yankin.

Ko a ranar Asabar, matasan sun tare hanyar, bayan samun labarin wasu direbobi na rastewa su bi ta garin Zuba su bi ta wajen, bayan rufe babbar hanyar da ta ratsa ta garin Kubwa.