✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Masu zanga-zangar EndSARS cinna wa shanu wuta

Masu zanga-zangar EndSARS sun cinna wa manyan motocin dauke da shanu wuta a Fagaba, Jihar Legas

Masu zanga-zangar EndSARS sun cinna wa wasu manyan motocin daukar dabbobi wuta a yankin Fagaba da ke Jihar Legas.

Mutanen sun sa wa tireloli biyu da ke makare da shanu wuta har ne a ranar Talata, ranar da aka gwamnatin jihar ta sanya dokar hana fita na sa’a 24 bayan zanga-zangar ta kara kazancewa a jihar.

Shugaban kunhiyar direbobi ta NURTW reshen kasuwar shanu ta Abbatuwa a Legas, Alhaji Muhammad Bello, ya shaida wa Aminiya cewa masu mutanen sun banka wa motocin wuta ne, bayan direbobin sun yi kokarin shiga da shanun cikin abbatuwa daga inda suke a tsaye domin gudun kada dokar hana fitar ta rutsa da su.

Ya ce masu zanga-zangar sun yi ta sarar shanun amma cikin yardar Allah an samu shanun da dama da ba su kai ga konewa ba.

Sai dai ya ce kawunan tirelolin da na wata da ta dauko tanki sun kone kurmus.