Mazauna garin Unguwar Magaji da ke Karamar Hukummar Chikun a Jihar Kaduna a ranar Asabar sun toshe babbar hanyar Kaduna zuwa Abuja suna zanga-zanga kan kisan wata yarinya da ’yan bindiga suka yi.
Yarinyar dai mai kimanin shekara 13 a duniya da wani mutum daya ne dai ’yan bindiga suka kashe har gida a yankin.
- Zaben Iran: Dan takara mai ra’ayin rikau na dab da lashewa
- Buhari ya nemi MTN ya rage kudin data da kira
Lamarin ya faru ne a daren Asabar lokacin da ’yan bindigar suka kutsa gidan mai unguwar yankin sannan suka yi awon gaba da iyalansa tare da wadansu mazauna kauyen.
Aminiya ta gano cewa mutanen yankin da lamarin ya faru da suka fusata da aika-aikar sun toshe babbar hanyar tun daga misalin karfe 8:30 na safiyar ranar ta Asabar.
Rahotanni sun ce matafiya da dama sun fuskanci matsala sakamakon yadda masu zanga-zangar suka toshe babbar hanyar ta ko ina, yayin da fusatattun matasa ke kiran gwamnati da ta samar musu da tsaro a yankin.
Matasan dai sun koka bisa yadda suka ce ’yan bindigar ke farautar su har gidajensu da ma gonakinsu.
Aminiya ta tuntubi Kakakin ’Yan Sandan Jihar, ASP Jalige Mohammed, amma bai amsa kiran ba.