Wasu mazauna Jihar Nasarawa sun mamaye kofar shiga majalisar dokokin jihar don nuna adawa da rikicin da ke faruwa a majalisar.
Masu zanga-zangar, karkashin kungiyar Concern Nasarawa Stakeholders Forum, dauke da kwalaye da rubuce-rubuce daban-daban, sun gargadi Gwamna Abdullahi Sule da kada ya haifar da rikici a jihar.
- Tinubu ya bayar da umarnin binciken hatsarin jirgin ruwan Kwara
- Mutum 10 sun shiga hannu kan zargin aikata laifuka a Bauchi
Sun yi kira ga Sufeto-Janar na ’yan sanda, Usman Baba, da ya sa Kwamishinan ’yan sandan jihar, Maiyaki Muhammed Baba ya binciki lamarin ba tare da nuna bangaranci ba.
Wasu rubuce-rubucen sun hada da: “Dole ne a ’yantar da Majalisar Nasarawa daga kangin bauta”, “’Yan sanda ba za su iya nuna bangaranci ba”, “Muna son zaman lafiya a Jihar Nasarawa”, da dai sauransu.
Da yake zanta wa da manema labarai a yayin zanga-zangar, wanda ya jagoranci zanga-zangar, David Manga, ya bayyana cewa bukatarsu shi ne yin bincike ba tare da nuna bangaranci ba.
Ya ce wannan hukunci na kwamishinan zai iya haifar da mummunan tashin hankali da rashin zaman lafiya a jihar.
Da yake kwantar wa masu zanga-zangar hankali, mataimakin kwamishinan ’yan sanda, Kingsley Emeka, ya shaida wa mazauna Nasarawa cewa za a isar da sakonninsu su yadda ya kamata ga Sufeto-Janar na ’yan sanda, inda ya bukace su da kada su tayar da hankali.
Idan za a tuna a satin da ya gabata Aminiya ta ruwaito yadda rikicin ya dabaibaye majalisar dokokin jihar inda aka samu shugabannin majalisar guda biyu, Daniel Ogazi da Balarabe Abdullahi.