Shugaba Muhammadu Buhari ya ce masu tayar da kayar baya za su iya samun magoya baya saboda abin da ya kira wa’azin da malaman da ke da tsauri suke yi wa jama’a.
Da yake jawabi daga kasar Jodan jiya a taron samar da tsaro wanda Sarki Abdullah na biyu ya shirya, shugaba Buhari ya yi kira da a dauki matakan da suka kamata a kawo karshen lamarin.