’Yan sanda sun cafke wasu matsafa a yayin da suke tsaka da yin tasfin kudi ta hanyar amfani da makara a garin Benin na Jihar Edo.
Aminiya ta gano cewa bayan shigar matsafan hannun ’yan sanda, na ukunsu, wanda fasto ne a wani cocin zamani ne ya tsere.
- ’Yan bingaida sun kona motocin matafiya 8 a Kaudna
- Kotu da daure dan kasar China kan yaga kudin Najeriya
Faston ya cika bujensa da iska ne bayan ya samu labarin cewa dubun abokan cin mushensa da suke tsafin kudin tare ta cika.
Matsafan wadanda shekarunsu 22 zuwa 24, sun shiga hannu ne a gidansu da ke yankin Irhirhi da ke kan titin Airport Road a garin Benin, hedikwatar Jihar Edo.
Makwabta ne dai suka tsegunta wa ’yan sanda, bayan sun ga matasan suna shigar da makara da mage da wasu kayan kulumboto tare da wasu mutane cikin gidan da suke haya.
Kakakin ’yan sandan Jihar Edo, Bello Kontongs, ya tabbatar da faruwar lamarin, da cewa matasan da aka kama ’yan asalin Jihar Delta ne.