Babban Hafsan Sojin Kasa na Najeriya, Laftanar-Kanar Faruk Yahaya, ya jadadda cewa sojoji ba za su ba da kofa ga duk wani tashin hankali ba a babban zaben 2023 ba.
Janar Yahaya ya bayar da tabbacin ne a wajen rufe taron farkon shekara na Hafsan Sojojin Kasa na 2022, inda ya yi alkawarin cewa Rundunar Sojin Kasa ta Najeriya za ta samar da tsaro na musamman.
- EFCC ta cafke Obiano a ranar da ya sauka daga kujerar gwamna
- NAJERIYA A YAU: Dalilan Da Mutane Ke Kashe Kansu Saboda Soyayya
“Hakan yana da mahimmanci musamman ganin yadda ayyukan da aka tsara na Jadawalin Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ke karatowa.
“Za mu ci gaba da samar da yanayi mai kyau na tsaro don gudanar da babban zaben ta hanyar taimakon hukumomin fararen hula,” in ji shi.
Babban hafsan sojin, ya bukaci sojoji da su ci gaba da nisanatar nuna bangaranci a yayin da suke gudanar da ayyukansu na wanzar da zaman lafiya da tsaron kasa.
Ya kuma umarce su da su ci gaba da kiyaye dokokin kare hakkin dan Adam da kundin tsarin mulki da kuma ka’idojin aiki a yayin gudanar da ayyukansu.
Yahaya ya kara da cewa munanan ayyukan ’yan ta’addan da ake fuskanta a kasar nan na dab da zuwa karshe.
Ya yaba wa sojojin kan kokarinsu da sadaukarwar da suke yi wajen tabbatar da samar da tsaro a kasar nan.
“Ina ba wa kwamandojin umarnin da su ci gaba da yin amfani da kyakkyawar alakar da ke tsakaninmu da jama’a don ci gaba da wayar musu da kai a kan ayyukanmu,” inji shi.