✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Masu shigo da jabun magunguna Kano sun gurfana a Kotu

Babbar Kotun Tarayya ta ba da belin wasu dillalai kan zargin shigo da jabun magunguna daga kasar waje da nufin sayawa a Kano.

Babbar Kotun Tarayya ta ba da belin wasu dillalai kan zargin shigo da jabun magunguna daga kasar waje da nufin sayarwa a Kano.

Hukumar Kula da Ingacin Abinci da Magunguna ta Kasa (NAFDAC) reshen Jihar Legas ce ta gurfanar da dillalan kan zargin aikata laifin a Jihar Legas, inda kotun ke zama.

Lauyan Hukumar NAFDAC, Barth Simon, ya shaida wa kotun cewa wadanda ake zargin — wani Shugaban Kungiyar Kamfanonin Dillancin Magunguna a Kano da abokan sana’arsa biyu — sun shigo da wasu jabun magunguna daga ketare domin kaiwa Kano su sayar, wanda hakan ya saba wa dokokin kasa.

Sai dai duk wadanda ake tuhumar sun musanta zargin, daga nan lauyansu Ikechukwu Anima, ya roki kotun ta ba da belin su.

Kotun ta amince da rokon nasa sannan ta ba da belin kowannensu a kan Naira miliyan bakwai, tare da masu tsaya musu da suka mallaki kwatankwacin kudaden.

Daga nan alkalin kotun, Ayokule Faji, ta dage sauraron shari’ar zuwa ranar 28 ga watan Maris, 2023.