✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Masu sana’ar gawayi ke kai wa ’yan bindiga bayanai —Basarake

Kamen da sojoji suka yi a yankin ya nuna cewa masu gawayin ne kashi 75% na mutanen da ke kai wa ’yan bindiga bayanai

Wani basarake a yanin Kachia da ke Jihar Kaduna ya zargin masu sana’ar gawayi a yankin da kai wa ’yan bindiga bayanan sirri.

Basaraken, wanda ya nemi a boye sunansa ya ce kamen da sojoji suka ya yi a yankin ya nuna cewa masu gawayin ne kashi 75% na mutanen da ke kai wa ’yan bindiga bayanai.

A hirarsa da wakilinmu ta wayar tarho a ranar Litinin, basaraken ya bayyana cewa galibin masu harkar gawayin suun zama ’yan aiken ’yan bindiga.

A cewarsa, ’yan bindigar sukan gindaya wa masu gawayin sharadi kafin su bar su su gudanar da sana’arsu a dazukan da ke yankin.

“Sharuddan sun hada da sayo musu kayan abinci da miyagun kwayoyi da sauran bukatu da kuma kawo bayanai ga ’yan bindigar.

“A wadannan dazuka da nake magana, babu manomin da ya isa ya je ya noma gonarsa, amma masu sana’ar gawayin suna zuwa su yi harkokinsu yadda suka saba,”  in ji shi.

Kokarinmu na samun karin bayani daga kakakin rundunar ’yan sadana a Jihar Kaduna, ASP Hassan Mansur, bai yi nasara ba.

Har har aka kammala wannan labarin jami’in bai ba da amsar sakon da muka aike masa ba kan wannan zargi.