Wasu da ake zargin masu safarar shinkafa ne daga wasu kasashe, sun kashe wani jami’in Kwastam da raunata wani a unguwar Asero a Abeokuta babban birnin jihar Ogun.
Rahotanni na bayyana cewa, Hukumar hana fasa-kwauri ta Najeriya, kwastam reshen jihar Ogun sun ce, a wani sintiri da jami’an suke a hanyar unguwar Asero akan dakile shirin safarar kaya ranar Lahadi .
An kashe jami’in hukumar Kwastam Hamisu Sani da ne lokacin da raunata sufeta Tijjani Michel lokacin da suke kokarin binciken motoci takwas da aka yi safarar shinkafa aka ajiye a unguwar Asero.