Tun daga lokacin da Gwamnatin Jihar Kano ta fitar da sanarwar dakatar da makarantu masu zaman kansu daga karin kudin makaranta a zangon karatu da za a shiga, masu makarantun ke ta guna-guni kan haka inda suka zargi gwamnatin da yi musu katsalandan a cikin harkokinsu.
Baba Abubakar Umar shi ne Babban Mataimaki ga Gwamnan Jihar, Alhaji Abba Kabir Yusuf kan makarantu masu zaman kansu, ya ce zai yi iya kokrinsa wajen ganin masu makarantun sun daina takura wa iyaye ta hanyar karin kudin makaranta ba tare da dalili ba.
- Ta’addanci: Ba don taimakon Majalisar Dinkin Duniya ba da mun banu — Tinubu
- ECOWAS ta musanta neman sojojin Nijar su mika wa farar-hula mulki nan da wata tara
Ya ce, “Za mu yi iya kokarinmu wajen ganin makarantun kudi sun yi abin da ya kamata. Za mu tabbatar da cewa ba su matsa wa iyayen yara wajen karin kudin makaranta koyaushe ba.
“Haka kuma a gefe guda muna damuwa da yadda suke tilasta wa iyaye a kan sayen kayan makaranta da kuma littattafai.”
Mashawarcin Gwamnan ya yi kira ga iyayen yara su rika biyan kudin makarantar ’ya’yansu a kan lokaci.
Alhaji Magaji Mahmud shi ne Sakataren Kungiyar Masu Makarantun kuma mamallakin Makarantar Nifolk, ya ce ba su ji dadin matakin gwamnatin ba inda ya roke ta ta sake duba wannan doka domin a cewarsa hana su yin karin kudin makaranta tamkar yi musu kanshin mutuwa ne.
“A gaskiya ba mu ji dadin wannan sanarwar da gwamnati ta fitar ba, duba da cewa wannan ce kadai hanyar da muke iya samun kudn gudanarwar makarantunmu.
“Idan kun yi la’akari da halin da ake ciki na yadda abubuwa suka yi tsada wanda kuma ya hada dukkan abubuwan da muke amfani da su a makarantun.
“Haka a gefe guda kuma akwai batun haraji da muke biyan gwamnati, akwai batun biyan albashin ma’aikatanmu da sauran bukatun yau da kullum.
“Muna kira ga gwamnati ta dube mu da idon rahama domin mu ma sana’a muke yi kamar kowane mutum da zai je kasuwa ya nemi halalinsa,” in ji shi.
Wata malama da ke da makaranta mai zaman kanta wadda ta nemi a boye sunanta ta bayyana cewa idan har gwamnati ta dage a kan wannan batu to gudanar da makarantun ba zai yiwu ba a wannan lokaci, duba da yadda abubuwa suka yi tashin gwaron zabo.
“Don haka muke kira ga gwamnatin ta sake duba wannan batu tare da kawo masalaha don warware batun cikin sauki,” in ji ta.
Malam Hamza Ahmad uba ne da ke da yara a makarantar kudi, ya shaida wa Aminiya cewa sun yi farin ciki da wannan mataki na gwamnati domin zai dan kawo sauki kan halin da a’lumma ke ciki.
“A gaskiya ba ni kadai ba iyaye da yawa mun yi maraba da wannan mataki na gwamnatin Kano domin abu ne da aka yi shi a kan gaba.
“Duba da halin da muka tsinci kanmu a kasar nan tun bayan janye tallafin man fetur. Yanzu ta abinci ake yi, ga kuma kudin makaranta da za a biya wa yara a yanzu da za a koma sabuwar shekarar karatu da ya hada da sayen littattafai da sauransu da ke da bukatar karin kudi da yawa.
“A hakan ma tunani mutum yake yi yadda zai biya ballantana idan aka ce an yi karin kudin,” in ji shi.
Wani mahaifi a nasa bangaren ya bayyana jin dadinsa game da matakin gwamnatin inda ya yi kira ga masu makarantun su yi hakuri da batun karin da suke shirin yi.
Ya ce, “Duk da cewa mun ji dadin wannan hukunci wanda ko shakka babu zai rage mana wata damuwar.
“A gefe guda kuma ina kira ga masu makarantun da su yi hakuri da ’yar karamar ribar da suke samu. Ba mu son yanayin da za a zo ana nuna wa juna yatsa a tsakaninsu da gwamnati.”
Makarantun kudi dai kullum kara habaka suke yi a ko’ina a Najeriya sakamakon halin ni-’yasu da makarantun gwamnati ke ciki, domin za a samu irin wadannan makarantu babu kujerun zama wasu rufin ajin ya lalace.
Kuma baya ga cinkoson dalibai a aji, a gefe guda makarantun na fama da rashin kwararrun malamai, lamarin da ke tilasta wa iyaye sa ’ya’yansu a makarantun kudi wadanda ake zargi da kara kudin makaranta a duk lokacin da suka bushi iska baya ga tilasta wa iyaye sayen littattafai da kayan makaranta daga hannunsu a farashinsu.