✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Masu kwacen waya sun raunata ma’aikaciyar Daily Trust a Kano

Mutane dai sun sami nasarar guduwa da wayarta da kudi N20,000 bayan sun yanke ta a hannu

Wasu ’yan daba a kan babur din Adaidaita Sahu da ake kyautata zaton masu kwacen waya ne sun tare ma’aikaciyar kamfanin jaridar Daily Trust a Kano, Zainab Yusuf, tare da raunata ta bayan sun kwace mata jaka.

Lamarin ya faru da Zainab, wacce ke aiki da sashen gudanarwa na kamfanin ne da safiyar Juma’a lokacin da take hanyar zuwa wajen aiki.

A cewarta, ’yan dabar su uku sun cim mata ne a babur din a daidai katangar rukunin katafarun kantinan Ado Bayero da aka fi sani da Shoprite, lokacin da take kokarin karawasa ofis bayan sauka daga Adaidaita Sahu.

Zainab ta ce, “Suna zuwa waje na sai mutum biyu suka sauka. Daya ya fara jan jakar dake hannu na nima ina ja yayin da shi kuma dayan yake ta kokarin sai ya caka min wuka.

Hannun ma’aikaciyar da ’yan dabar suka yanka bayan kwace mata jaka
Hannun ma’aikaciyar da ’yan dabar suka yanka bayan kwace mata jaka

“Da farko fuska ta ya dinga hari ina kaucewa, sai ya fara kokarin soka min a gefen cikina yayin da na fadi kasa wanwar duk da haka ban saki jakar ba ina ta gocewa.

“Yayin da naga ya fara harin wuyana ne na saka hannu na. Hakan ta sa ya yanke min dan yatsa ya kuma yanke ni a hannu da kafa suka tafi da jakar,” inji ta.

Sai dai ta ce ’yan sa’o’i bayan faruwar lamarin, an tsinci jakar tata a gefen titi a unguwar Sharada.

Wadanda suka tsinci jakar sunyi amfani da shaidar wurin aikin ta domin tuntuba da mayar mata da kayan ta.

Sai dai ta ce barayin sun yi awon gaba da wayar ta kirar iPhone da kudi kimanin Naira 20,000.