✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Masu kashe-kashe a Kudu maso Gabas ’yan kabilar Ibo ne — Gwamnan Anambra

Gwamna ya ce gwamnatinsa za ta sa kafar wando daya da su

Gwamna Charles Soludo na Jihar Anambra, ya ce yawancin ’yan bindigar da ke haddasa yawaitar tashe-tashen hankula da kashe-kashe a jihar ’yan kabilar Ibo ne.

Da yake magana a lokacin da ya ke ayyana dokar hana fita a Kananan Hukumomi bakwai na Jihar, Soludo ya yi Allah-wadai da yadda ’yan awaren IPOB ke ci gaba da kai hare-hare.

Ya ce dokar za ta ci gaba har sai an samu zaman lafiya.

“Bari mu fayyace yadda abin yake. Wadannan miyagu da ke haddasa tashe-tashen hankula a Anambra,  na kungiyoyi da gungun ’yan ta’adda ’yan kabilar Ibo ne (masu rinjaye a wasu Jihohin Kudu maso Gabas) wadanda ainihin manufarsu ita ce cin hanci da rashawa da kuma ayyukan da suka shafi tsafi a yankin.

“Abin takaici, kowane gungun masu aikata laifuka (ciki har da kungiyoyin asiri) kowanensu na da’awar kare hakkin jama’a, don haka da wuya a banbance tsakanin na gari da mugu. Abin takaici kuma, masu aikata laifuka sun rinjayi masu fafutukar,” inji shi.

A cewar Gwamnan, Anambra ce aka fi kai wa hari domin ita ce wurin da ya fi samun kudin fansa idan an yi garkuwa da mutane.

Kazalika, ya ce suna ikirarin cewa suna gwagwarmaya ne don jama’a, amma suna kashe al’ummarsu, suna lalata dukiyoyi tare da hana yara zuwa makaranta.

“Mene ne alakar tayar da hankali da sace-sacen mutane da suka hada da sace fasto?,” inji Soludo.

Sai dai Gwamnan ya ce ’yan ta’addan ba su yi nasara ba, domin Gwamnatin Jihar za ta sa kafar wando daya da su.